Yanzu Yanzu: Zanyi murabus nan da mako guda – Fayemi
- Ministan ma’adinai, Dr. Kayode Fayemi yace zai yi murabus daga matsayinsa nan da mako guda
- Fayemi na neman kujerar gwamnan jih Ekiti karkashin APC a yanzu haka
Ministan ma’adinai, Dr. Kayode Fayemi a ranar Laraba, 16 ga watan Mayu yace zai yi murabus daga matsayinsa nan da mako guda.
Fayemi, wanda ke neman kujerar gwamna na jihar Ekiti karkashin jam’iyyar All Progressives Congress ya zanta ne da manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja.
KU KARANTA KUMA: Rikici ya barke tsakanin matasan Binanchi da na Iraki a jihar Sokoto (hotuna)
Yace akwai aiki sosai da zasuyi sannan kuma shi da sauran masu takara na kalon wannan zabe mai zuwa a matsahanyar ceto.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng