Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Jigawa a yau

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Jigawa a yau

Shirye shirye sun kammala tsaf na ziyarar aiki ta yini biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar Jigawa a yau Litinin, 14 ga watan Mayu.

A sanarwar da sashen tarban baki na gidan gwamnati ta bayar tace ana sanya ran shugaban kasar zai sauka a filin jirgin saman Dutse da misalin karfe goma na safe inda zai wuce zuwa garin Auyo domin kaddamar da aikin noman rani.

Sannnan daga bisani ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje a fadarsa.

Shugaban zai kuma bude aikin hanyar Tasheguwa zuwa Guri da kuma Guri zuwa Abunabo.

Daga bisani Buhari zai dawo Birnin jiha Dutse inda zai kai ziyarar ban girma ga mai martaba sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi .

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Jigawa a yau
Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Jigawa a yau

Sannan shugaban zai ziyarci unguwar Dasina inda zai bude tashar bada ruwansha mai aiki da hasken rana kana daga bisani a gudanar da taron masu ruwa da tsaki da kuma liyafar cin abinchi a gidan gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar SERAP ta kai shugaba Buhari kara a Majalisar Dinkin Duniya sakamakon sabawa hukuncin kotu

A rana ta biyu ana sa ran shugaban zai kaddamar da baje kolin kayayyakin amfanin gona, sai kuma gangamin da magoya bayan jamiyyar APC suka shirya masa a filin taro na Mallam Aminu Kano dake birnin Dutse.

Bayan kammala wadannan ayyukan ne shugaban kasa zai bar Dutse zuwa Birnin tarayya Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel