Amarya ta gudu bayan mijinta ya kasa hada kayan lefe
Jami’an ‘yan sanda a karamar hukumar Suleja, dake Jihar Nige sun damke iyayen wata amarya sakamakon kin tarewa a gidan mijin, da aka daura musu aure.
Ango mai suna Shuaibu Dauda ne ya kai karar, ya ce sa’o’i kadan bayan daura aure, an nemi amarya ko sama ko kasa an rasa.
Wannan dalili ne ya sanya angon kuma kai karar surukan na sa, su kuma ‘yan sanda su ka kama su.
Babban jami’in ‘yan sanda na Kaduna Road, Aliyu Lawal, shi ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai wannan bayani.
Ya shaida masa cewa yayin da mata ‘yan daukar amarya suka rangada kwalliya suka nufi gidan iyayen amarya, sai suka nemi amarya suka rasa.
Sufeto Lawal ya ce ganin yadda iyayen amarya suka rika jan-kafa wajen fitowa iyayen ango da amarya, hakan ya kai ga yin rikici a tsakanin bangarorin biyu.
Wannan ne ya sa aka kamo iyayen amarya din a ranar 6 ga watan Mayu, sannan kuma aka hada da waliyin ta.
Sai dai kuma ya ce an bada belin su bayan kwana daya a ranar 7 ga watan Mayu.
Da aka tuntube shi, Abubakar Haruna, ya shaida cewa ya bada auren ‘yan mata biyu ne a rana daya.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan shi’a dake zanga-zanga sun kora jami’an yan sanda a Abuja
Ya bada auren Fiddausi ga Dauda, ita kuma Saliha ga Muhammadu Murtala.
Ya ci gaba da cewa tun kafin a daure, Dauda da Muhammadu Murtala sun yi alkawarin kawo sadaki da kayan lefe kamar yadda addinin Musulunci da al’ada su ka tanadar.
“Amma ana gama shafa Fatiha sai Dauda ya ce shi fa ba zai iya kawo kayan lefe ba."
Ya ce Dauda ya harzuka har ya dauko abokan sa suka zo gidan sa suka yi masa rashin mutunci, suka kuma daki matar sa mai suna Bayi.
“Ba ma ta karan kan mata ta ba, har mata ‘yan biki sai da aka yi wa dukan tsiya, kuma su ka rika yin kutubal da abincin biki."
Malam Haruna ya ce ‘yan sanda karya suke yi da suka ce wai sun kama shi da matar sa da Umar Haruna Waliyin amarya saboda sun tayar da fitina.
Ya ce ‘yan sanda ba su kama wadanda suka tayar da fitina a gidan sa ba, sai ma suka ce masa wai ya biya ango N260,000 tunda amarya ta ki tarewa.
KU KARANTA KUMA: Buhari yayi ta’aziyya ga Fasto Bakare akan mutuwar mahaifiyarsa
Saboda ya ce wa ‘yan sanda ba shi da wadannan makudan kudi ne suka yi masa barazanar kulle shi. Amma Washegari da safe aka bada belin su.
A daidai lokacin da ake rubuta wannan labari, Fiddausi ta ki tarewa, ta na gidan iyayen ta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng