Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Shugaban kungiyar sabuwar APC na kasa, Buba Galadima ya caccaki shugabannin jam’iyya mai mulki, inda ya bayyana su a matsayin bayi dake kokarin rufe ubangidansu a waje. Ya yi Magana a jiya da daddare a shirin siyasa a yau.
Rundunar yan sandan jihar Niger sun kama wasu yan fashi biyu da suka kai hari ga ayarin motocin dake dauke da kayayyaki daga kasuwar Kokongi ta hanyar kauyen Wawa dake karamar hukumar Borgu dake jihar ta Niger.
Samuel Aruwan, kakakin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa babu wani dan takarar gwamnqa a jihar da zai iya kayar da El-Rufai a 2019. Cewa babu dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna da za su iya kayar da shi.
Matasa a jihar Kano karkashin wata kungiyar siyasa mai suna ‘Ranar Wanka Buhari/Ganduje Progressive Group’, sun kammala shirye-shirye don yin gangamin matasa miliyan uku a jihar domin nuna hamayya da ayyukan siyasa na R-APC.
Rahotanni dake zuwa mana daga masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood ya nuna cewa Kyakyawar alaka ta kullu tsakanin jaruman Fim Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau sosai a yanzu. Hakan ya biyo bayan rashin fahimta tsakanins
Wani dan majalisan jihar Plateau, Ahmed Maje, ya bugi kirji ya zargi wasu yan siyasa da hannu a cikin kashe-kashen Jos da rikicin da akayi kwanan nan. Maje ya bayyana cewa ya sanya rayuwarsa cikin hatsari ta hanyar bayyana wannan.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, ya sanar da cewa yana nan yana nazari kan ficewa jam'iyyar APC da kuma yiyuwar komawarsa jam'iyyar PDP. Tsohon kakakin majalisar wakilan kasar yana cikin mambobin sabuwar PDP.
Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya yi kira ga a binciki mutuwar yan sanda bakwai da aka rahoto cewa yan bindiga sun kashe a shataletalen Galadimawa, dake Abuja a ranar Litinin, 2 ga watan Yuli.
Manyan shugabannin siyasa daga jihar Bauchi sun rubuta wasikar korafi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari gabannin zaben 2019, sunce lallai yayi aiki da dansu, kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara kamar yadda suka yi a 2015.
Aisha Musa
Samu kari