Son kyautatawa mata ta ne ya kai ni ga sata – Mai laifi
Rundunar yan sandan jihar Niger sun kama wasu yan fashi biyu da suka kai hari ga ayarin motocin dake dauke da kayayyaki daga kasuwar Kokongi ta hanyar kauyen Wawa dake karamar hukumar Borgu dake jihar.
Jami’an yan sanda da aka tura New Bussa ne suka kama masu laifin, Jariri Chede, 25, da Janya Shehu, 20, bayan sun yiwa wani Sunday Ishaya a kauyen Kkongi fashin kudinsa da sauran muhimman abubuwa.
An tattaro cewa wanda akayiwa fashin na tuki a hanyar Kokongi zuwa kauyen Wawa lokacin day an fashin suka far masa suka sace masa N70,000 da wata wayar Tecno da farashin ta ya kai N73,000.
Masu laifin sun tafi da kwalayen lemun maye 2 wanda farashin su ya kai N9,000 da kuma kwalin lemun snuff wanda farashin say a kai N2,000.
Masu fashin sun fashin sun fito daga daji sannan suka kai hari ga mutumin da bindiga da adduna wanda das u ne suka ji masa raunuka, inda suka barshi kwance cikin jini.
Shehu, wanda yayi aure kwanan nan, ya bayyana cewa ya shiga kungiyar fashin ne saboda yana bukatar kudin da zai kula da matar sa.
KU KARANTA KUMA: Kun ba da mu: Jokolo ya soki Manyan Arewa na yin shiru a Gwamnatin Buhari
Da aka tambaye shi kan yadda matarsa da yan uwansa za su ji, Shehu ya ce, “babu shakka mata ta za ta ji babu dadi amma na aikata annan laifi ne domin ita, sannan a bangaren iyayena, na ba su kunya sannan ina rokonsu da su yafe mun.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng