Hunkuyi, Ashiru, da Sani ba za su taba kamo kafar El-Rufai a 2019 ba - Aruwan
Samuel Aruwan, kakakin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa babu wani dan takarar gwamnqa a jihar da zai iya kayar da El-Rufai a 2019.
“Babu daya daga cikin yan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna da za su iya kayar da Malam (El-Rufai).”
Kawai suna ra’ayin son kasancewa a wajen ne amma ba su da nufin kawo cigaba, manufofi masu inganci don cigaban jihar da sauransu.
Koda ya ke sauran yan takara da dama basu kaddamar da kudirinsu a bayyane ba, yan siyasan da ake ganin suna burin son shugabantar Kaduna sune, sanata Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi; da kuma shahararren dan siyasan Kaduna, Isa Ashiru. Sauran sun hada da tsohon gwamna, Mukhtar Yero da Muhammad Bello.
KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Kyakyawar alaka ta kullu tsakanin Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau a yanzu
Da yake Magana a wani taron karama juna sani tare da yan jarida a Kaduna a ranar Alhamis, Mista Aruwan yace ya yi imani babu wani dan takara da zai iya kamo kafar El-Rufai ta ganin hangen nesa, shugabanci, ayyukan cigaba da jajirjewa wajen bautawa tare da kawo cigaba a jihar da kuma mayar da hankali kan aiki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng