Ina N450bn Ta Shiga? Atiku Ya Sake Dauko Magana Mai Girma kan Tallafin Manoma a Najeriya
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Tinubu da yaudarar manoma da ikirarin cewa ta ware N450bn domin tallafa musu
- Ya nemi gwamnati ta bayyana sunayen waɗanda suka amfana, kuɗaɗen da aka fitar da kuma tasirin tallafin ga noman shinkafa a cikin gida
- Atiku ya ce rahotanni sun nuna cewa sama da masana’antun sarrafa shinkafa 90 daga cikin 260 a Najeriya sun dakatar da aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da yaudarar manoman Najeriya.
Atiku ya zargi gwamnati mai ci da ikirarin ware biliyoyin Naira domin tallafa wa harkokin noma, alhali masana’antun sarrafa shinkafa na fuskantar rufewa.

Source: Facebook
Atiku ya ƙalubalanci gwamnatin tarayya da ta gabatar da hujjojin ikirarin cewa ta ware N450bn domin tallafa wa manoma, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta buɗe shirin tallafin teloli a Najeriya, kowane mutum zai iya samun N5m
Ya nemi ta bayyana sunayen waɗanda suka amfana, adadin kuɗin da aka biya a zahiri da kuma tasirin tallafin ga noman shinkafa a cikin gida.
Atiku ya bakado batun tallafin N450bn?
Atiku ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa kan harkokin dabarun sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Juma’a, 27 ga Nuwamba, 2026.
Wazirin Adamawa ya yi tambaya kan ikirarin gwamnatin cewa ta ware N250bn domin tallafa wa ƙananan manoma, yayin da aka ware wasu N200bn domin shirin tabbatar da mafi ƙarancin farashin amfanin gona.
Ya ce sanar da cewa an ware kuɗi bai wadatar ba idan ba a bayyana wa jama’a adadin kuɗin da aka fitar a zahiri ba, waɗanda suka amfana, irin amfanin gonar da aka saya da kuma farashin da aka biya manoma.
Atiku ya ce:
“Wannan wata dabara ce da gwamnatin Tinubu ta saba amfani da ita: ta sanar da ware makudan kuɗi, ta ɓoye gazawarta, sannan ta kira duk wanda ya nemi ganin shaidar biyan kuɗin marar godiya. ’Yan Najeriya sun gaji da yaudararsu.”

Kara karanta wannan
Atiku ya taso Tinubu da NNPCL gaba a yi bayanin inda Naira tiriliyan 1.4 ya maƙale
Ya ƙalubalanci gwamnati da ta bayyana manoman da suka karɓi kuɗin da kuma masana’antun sarrafa shinkafar da suka sake buɗewa sakamakon tallafin, yana mai cewa dole ne a tabbatar da ikirarin N450bn da hujjojin da za a iya tantancewa.

Source: Getty Images
Masana’antun shinkafa na rufewa
Atiku ya kuma yi tsokaci kan wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa, wanda ya nuna cewa sama da masana’antun sarrafa shinkafa 90 daga cikin 260 da ke Najeriya sun dakatar da aiki.
A cewarsa, masana'antun sun daina aiki ne saboda ƙarancin samfarerar shinkafa da ake nomawa a cikin gida, hauhawar kuɗaɗen samarwa da kuma gasar shinkafar da ake shigowa da ita daga ƙasashen waje mai rahusa.
Atiku ya amince da lakabin Daddy Subsidy
Kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya amince da sunan “Daddy Subsidy” da magoya bayansa suka rada masa gabanin zaben 2027.
Atiku wanda ke neman takarar shugaban kasa, ya ce sauƙi na tafe wa ’yan Najeriya, inda ya yi alƙawarin dawo da sauƙin rayuwa a ƙasar idan ya samu nasara a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng