‘Dan Kwallo Ya Yi Hadarin Mota a kasar Sifen Ana Shirin Buga Wasan Barcelona

‘Dan Kwallo Ya Yi Hadarin Mota a kasar Sifen Ana Shirin Buga Wasan Barcelona

  • ‘Dan wasan Deportivo La Coruña, Pierre-Emerick Aubameyang, ya yi hatsarin mota da safiyar Alhamis a kan hanya a kasar Spain
  • Yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa atisaye, motarsa kirar Ferrari F12 N-Largo ta yi karo da wata mota kirar BMW X1 wanda ta kife
  • An yi dace shi da dayan direban sun tsira ba tare da rauni ba kuma Aubameyang ya ci gaba da shirye-shiryen karawa da Barcelona

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Spain - Pierre-Emerick Aubameyang ya yi hatsarin mota da safiyar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026, a hanyarsa ta zuwa atisaye a kulob dinsa.

Hakan ta faru ne a kan hanyarsa ta kungiyarsa ta Deportivo La Coruña gabanin karawarsu da Barcelona da za a yammacin ranar Lahadi.

'Dan wasa Pierre-Emerick Aubameyang ya gamu da hadari

Babu wanda ya samu mummunan rauni a sakamakon hadari, kuma dan wasan ya halarci atisayen da aka tsara a cewar rahoton Goal.

Kara karanta wannan

Wanda ya fara bankado zargin alakar Dan Bello da Seyi Tinubu yana cikin barazanar kisa

Hatsarin ya auku ne da misalin karfe 9:23 na safe a kilomita 16 na babbar hanyar AP-9 da ke yankin Piadela a kusa da birnin Betanzos.

Inda abin ya faru yana cikin yankin Arewa maso yammacin Spain, kasar da Pierre-Emerick Aubameyang yake taka leda a yanzu.

Yadda Pierre-Emerick Aubameyang ya yi hadarin

Aubameyang mai shekaru 37 a duniya yana tuka mota kirar Ferrari F12 N-Largo ne lokacin da suka yi karo da motar BMW X1 kan titi.

Wannan lamari ya sa motar BMW din ta kife kafin motar daukar kaya ta janye ta daga kan titi.

Jami'an tsaro na Civil Guard da jami'an kashe gobara da na agajin gaggawa sun isa wurin, kuma duk wadanda ke cikin motocin sun tsira.

Rahotanni daga kasar Turan sun tabbatar da su biyun sun fito lafiya ba tare da wani mugun rauni ba.

'Dan wasan ya yi atisaye a Deportivo

Bayan hatsarin, Aubameyang ya ci gaba da tafiya a motarsa zuwa sansanin atisayen Deportivo na Cidade Deportiva de Abegondo a ranar.

Yahoo Sports ta ce tsohon ‘dan wasan na Barcelona ya shiga kulob dinsa kuma ya samu atisayen kungiyar a kan lokaci yadda aka tsara.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kai wa fitacciyar 'yar TikTok kuma 'yar Kwankwasiyya hari a Kano

Da yake magana bayan isowarsa, dan wasan na kasar Gabon ya ce ‘dan tsoro ne kawai ya shiga da motocin nasu suka yi karo a kan hanya.

Aubameyang yake cewa abu mafi muhimmanci shi ne shi da dayan direban sun tsira lafiya.

"Irin waɗannan abubuwa sukan faru a rayuwa. Abu mafi muhimmanci shi ne ɗayan mutumin da abin ya shafa a hatsarin yana cikin ƙoshin lafiya, ni ma kuma ina lafiya."

- Pierre-Emerick Aubameyang

Yadda Aubameyang ya so kungiyar Real Madrid

A shekarar 2016 aka samu rahoto cewa Pierre-Emerick Aubameyang ya sake nanata burinsa na buga wa Real Madrid wasa a rayuwar shi.

'Dan wasan gaban ya yi wa kakansa alkawarin taka leda a Santiago Bernabéu, daya daga cikin mafi girman kungiyar kwallon kafa a duniya.

A wancan lokaci, Dortmund ta ki sayar da shi ga Man City da Inter Milan. Daga baya dai an ji yadda ya buga wa Arsenal kafin ya dawo Sifen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng