Nigerian news All categories All tags
Ina shawara kan makomata a APC – Tambuwal

Ina shawara kan makomata a APC – Tambuwal

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, ya sanar da cewa yana nan yana nazari kan ficewa jam'iyyar APC da kuma yiyuwar komawarsa jam'iyyar PDP.

Tsohon kakakin majalisar wakilan kasar yana cikin mambobin jam'iyyar APC da ake kira 'yan sabuwar PDP da ke takun-saka da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamna Tambuwal ya bayyanawa majiyarmu cewa yana nan yana tunani tare da jama'arsa akan da ko zai ci gaba da kasancewa a jam'iyyar APC ko kuwa akasin haka.

Gwamnan kuma bai musanta yiyuwar sake koma wa babbanj jam'iyyar adawa ta PDP, bayan an tambaye shi ko PDP zai koma kamar yadda ake rade-radi.

Ina shawara kan makomata a APC – Tambuwal

Ina shawara kan makomata a APC – Tambuwal

"Ba a yin siyasa a boye, duk abin da muka tanada muka yi shawara a kan shi, ba da dade wa za mu fito da shi," in ji Gwamna Tambuwal.

Daga nan ya ce bayan sun kammala cimma matsaya zai fito ya fada wa duniya.

Gwamnan na Sakkwato ya fadi hakan ne a wani taron da BBC ta shirya a birnin Legas a kudancin Najeriya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa ‘Yan bangaren R-APC wadanda su ka bangare daga Jam’iyyar APC mai mulki za su gamu da cikas bayan ‘Yan Majalisa da-dama sun yi zaman su a APC.

KU KARANTA KUMA: Sanatan Jihar Kaduna na kokarin ganin an kafa sabuwar Jami’a a Zaria

Da alama dai kokarin da ake yi na kawo rabuwar kai a Jam’iyyar APC mai mulki ba zai kai ko ina ba don kuwa Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu manya a Jam’iyyar APC a kasar sun nuna cewa babu inda za su tafi.

Daga cikin wadanda su ka nuna ba za su bi tafiyar R-APC na sababbin ‘Yan tawaren ba akwai manyan Sanatoci irin su Abdullahi Adamu; Aliyu Wammako; Danjuma Goje; Adamu Aliero; da kuma Sanata Kabiru Gaya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel