Ni ne na fi kowa iya ado a nahiyar Afirka – Wani mutum

Ni ne na fi kowa iya ado a nahiyar Afirka – Wani mutum

Wani mutumin kasar Kenya ya yi ikirarin cewa ya fi kowa iya ado da kwaliyya a nahiyar Afrika.

A cewar mutumin ya mallaki kwata sama da 160, sannan kuma yana da hula fiye da 300.

Ba wannan kadai ba mutumin wanda ya kasance dan kasar Kenya ya jadadda cewa yana da takalma kala-kala sun fi 200.

Ya ce ba ma a Afrika kadai ba, shi yana ganin ya fi kowa iya gayu a duniya. Domin idan zai saka kaya yakan saka komai kalar kayan ne hatta da zobunan hannu, gidan waya, dama tsunman goge gumin sa.

Ni ne na fi kowa iya ado a nahiyar Afirka – Wani mutum

Ni ne na fi kowa iya ado a nahiyar Afirka – Wani mutum

A cewar bawan Allan: "Lokacin da na zo Nairobi, babban birnin tarayyar Kenya, riga daya ne dani, don haka mutane ke yi mun dariya, saboda sun san mahaifina talaka ne.

KU KARANTA KUMA: 2019: Doyin Okube ya shawarci Saraki da ya tsaya takarar shugabancin kasa

"Sai na roki Allah ya bani abun da zan yi daban da mutane, shine ya amsa addu'a na."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel