Majalisar Borno ta tsayar da Shettima takarar Sanata

Majalisar Borno ta tsayar da Shettima takarar Sanata

'Yan majalisar dokokin jihar Borno sun bukaci Gwamnan jihar, Kashim Shettima da ya fito takarar kujerar dan majalisar Dattawa na Borno ta Tsakiya tunda zai kammala zangonsa na shekaru takwas a matsayin gwamna.

Yan majalisan da aka zaba karkashin lemar jam’iyyar APC sun ce, ya zama dole Gwamnan ya fito takara don al'ummar mazabarsa sun amfana da irin kwarewarsa da iliminsa.

Majalisar Borno ta tsayar da Shettima takarar Sanata

Majalisar Borno ta tsayar da Shettima takarar Sanata

Kakakin majalisar jihar, Lawal ya bayyana hakan a jiya a gaban wasu mambobin mjalisar jihar yayinda wata kungiyar siyasa mai suna Kashim Shettima Youth Mobilization (KSYM), karkashin jagorancin wani jigon APC, Al-Amin Mustapha Alkali syka halarci wani taro da aka yi a Maiduguri.

KU KARANTA KUMA: Muna da hujja akan yan siyasar dake da hannu a kashe-kashe – Fadar shugaban kasa

Tun da farko dai, Gwamnan Shetiima ya fito fili ya nuna cewa idan har wa'adinsa ya cika, zai koma aikin koyarwa ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel