Matasa miliyan 3 za su yi gangami a Kano don nuna hamayya da R-APC
Matasa a jihar Kano karkashin wata kungiyar siyasa mai suna ‘Ranar Wanka Buhari/Ganduje Progressive Group’, sun kammala shirye-shirye don yin gangamin matasa miliyan uku a jihar domin nuna hamayya da ayyukan siyasa na gammayar kugiyar da sabuwar APC wato Reformed APC (R-APC).
Da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis, shugaban kungiyar, Alhaji Bala Salihu Dawaki, ya ce kwanan nan za su gudanar da tattakin, a cewarsa, an kammala shirye-shirye.
Dan siyasan wanda aka Haifa a jihar Abia ya kuma bayyana cewa bashi da tabbacin ko maganin Kwamrad Adams Oshiomhole zai warkar da raunukan dake zukatan miliyoyin mambobin APC wadanda suka jajirce a jam’iyyar a baya.
KU KARANTA KUMA: Ina shawara kan makomata a APC – Tambuwal
A baya Legit.ng ta rahoto cewa ‘Yan bangaren R-APC wadanda su ka bangare daga Jam’iyyar APC mai mulki za su gamu da cikas bayan ‘Yan Majalisa da-dama sun yi zaman su a APC. KU
Da alama dai kokarin da ake yi na kawo rabuwar kai a Jam’iyyar APC mai mulki ba zai kai ko ina ba don kuwa Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu manya a Jam’iyyar APC a kasar sun nuna cewa babu inda za su tafi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng