An Jefi Paparoma Leo a Fuska yayin Gaisawa da Mutane, Ya Yi Martani

An Jefi Paparoma Leo a Fuska yayin Gaisawa da Mutane, Ya Yi Martani

  • Wani mutum ya jefi Paparoma Leo XIV da carbi inda suka same shi a fuska yayin da yake gaishe da mabiya addinin Kirista a Peru
  • Lamarin ya faru ne yayin da Paparoma ke cikin motarsa ta musamman a filin jirgin saman Las Palmas da ke Lima
  • Duk da faruwar lamarin, Paparoma Leo bai samu rauni ba, kuma ya ci gaba da gudanar da sauran ayyukansa kamar yadda aka tsara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Peru - Paparoma Leo XIV ya gamu da wani abin mamaki bayan an jefi shi da carbi, waɗanda suka same shi a fuska yayin da yake gaishe da dubban Kiristoci a ƙasar Peru da ke Kudancin Amurka.

Wani bidiyo da aka ɗauka lokacin faruwar lamarin ya nuna yadda Paparoma ke daga hannu yana gaishe da mutane daga cikin motarsa ta musamman, kafin ƙwallayen addu'ar su same shi a fuska.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tausaya wa matasan da aka kama kan jifan motocinsa a masallacin Juma'a

An jefi Paparoma Leo a Peru
Shugaban darikar Katolika ta duniya, Pope Leo. Hoto: Getty Images.
Source: Twitter

Rahotanni daga PM News sun bayyana cewa Paparoma mai shekaru 71 ya yi wani motsi na nuna jin zafi tare da shafa idonsa bayan abin ya same shi, amma ya ci gaba da gaishe da jama'ar da suka taru domin ganinsa.

Yadda lamarin ya faru

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin lokacin da Paparoma Leo ya isa filin jirgin saman sojoji na Las Palmas da ke birnin Lima domin gudanar da taron addu'ar bankwana, wanda ya kawo ƙarshen ziyararsa ta kwanaki 12 a Kudancin Amurka.

Jami'an tsaro sun ƙara tsaurara matakan kariya yayin da motar Paparoma, wadda aka ƙera musamman domin kare shi daga barazanar tsaro, ta rage gudu a hanyarta ta zuwa wurin taron.

Duk da faruwar lamarin, Paparoma bai samu wani rauni da aka tabbatar ba, kuma ya ci gaba da gudanar da shirye-shiryensa.

A cikin wa'azinsa, ya gode wa al'ummar Peru bisa kyakkyawar tarbar da suka yi masa a tsawon kwanaki shida da ya shafe a ƙasar, inda ya taɓa gudanar da muhimman ayyuka a rayuwarsa ta addini. Paparoma ya shahara wajen cafke kyaututtuka.

Kara karanta wannan

'An jikkata mutane da dama a harin da aka kai wa Kwankwaso a Kano,' Obi

Wasu sun jefi Paparoma Leo a fuska
Jagoran darikar Katolika ta duniya, Pope Leo. Hoto: Alfredo ESTRELLA / AFP via Getty Images.
Source: UGC

Ana yawan jefawa Paparoma abubuwa

Paparoma Leo ya shahara wajen saurin motsawa da cafke kyaututtukan da mutane ke jefa masa yayin tarukan da yake halarta.

Rahoton ya bayyana cewa Paparoma, wanda yake sha'awar wasan Tennis, ya taɓa cafke kayan wasa da tutoci da magoya bayansa suka jefa masa yayin da yake gaishe da jama'a.

Haka kuma, a wani lokaci ya tsaya domin karɓar pizza da wasu mutanen Chicago, garinsu, suka miƙa masa yayin wani taro a dandalin St Peter's Square.

Sai dai ba dukkan ƙoƙarinsa na cafke abubuwan da ake jefowa gare shi ne ke yin nasara ba.

A wani taro da ya halarta a Rome, ya taɓa bugun wani mai ɗaukar hoton Vatican da ke bayan motarsa yayin da yake ƙoƙarin cafke wani abu da aka jefa masa. Daga baya ya nemi afuwar mai ɗaukar hoton.

An ƙi rashin lafiyar Paparoma Leo

Mun ba ku labarin cewa Paparoma Leo XIV ya kamu da cutar kansa a huhu, amma likitoci sun yi nasarar yi masa tiyata domin cire ɓangaren huhunsa na dama da cutar ta shafa.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi tsanani har kotu tana yi wa ministan Tinubu barazana da dauri a kurkuku

Fadar Vatican ta bayyana cewa an yi wa Paparoma mai shekaru 71 tiyatar na tsawon mintuna 90 a ranar Talata a asibitin Gemelli da ke Rome.

Rahoton likitoci ya ce an yi nasarar tiyatar ba tare da samun wata matsala ba, kuma ana sa ran Paparoma zai shafe kusan mako guda a asibiti domin ya murmure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.