Ba za mu barwa bayinmu APC ba – Shugaban R-APC
Shugaban kungiyar sabuwar APC na kasa, Buba Galadima ya caccaki shugabannin jam’iyya mai mulki, inda ya bayyana su a matsayin bayi dake kokarin rufe ubangidansu a waje.
Ya yi Magana a jiya da daddare a shirin siyasa a yau wanda gidan talbijin din Channels ke haskawa.
Ya ce: “Bana bukatar yin Magana da yawa wajen nuna matsayina a matsayin dan jam’iyyar APC. Wadanda ke cewa suna kokwanto kan kasancewa dan APC ba lallai ne su sani ba saboda lokacin da muke kokarin kafa APC, bamu kansu ba. Basa ko ina. Don haka ta yaya za su sani? Su je hukumar zabe sannan su duba sa hannu. Buba Galadima ne mutun na uku da ya sanya hannu a takardan kafa jam’iyyar.
Kan cewa ko gamayyar kungiyarsa za su bar APC, ya ce hakan ba zai taba yiwuwa ba ace maigida ya barwa bayinsa gidansa.
KU KARANTA KUMA: Son kyautatawa mata ta ne ya kai ni ga sata – Mai laifi
Ya kuma karyata rahoton cewa wasu masu son ruguza jam’iyya mai mulki ne ke daukar nauyin kungiyarsa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng