Dan majalisa Ahmed Maje ya nuna yan siyasa a kisan Plateau, ya ce lallai yana da hujja (bidiyo)
Wani dan majalisan jihar Plateau, Ahmed Maje, ya bugi kirji ya zargi wasu yan siyasa da hannu a cikin kashe-kashen Jos da rikicin da akayi kwanan nan. Maje ya bayyana cewa ya sanya rayuwarsa cikin hatsari ta hanyar bayyana wannan babban maganan, ya kara da cewa yana da hujja akan zargin sa.
Ahmed Maje dan majalisar wakilai daga mazabar Wase, jihar Plateau ya zargi wasu yan siyasa da hannu a kisan kiyashin da ake zargin wasu makiyaya da aikatawa. Maje yace yana sane da cewar ya sanya kansa cikin babban hatsari da yayi irin wannan zargin tunda yana da hujjar kare kansa akai.
Dan majalisan ya bayyana cewa yana dauke da takardu don nuna cewa yan siyasa sun shigo da makamai da alburusai cikin kasar wanda hukumar kwastam din Najeriya basu kama ba a iyakokin kasar.
Dan majalisan yayi wannan zargi ne a zaman majalisa. Ga bidiyon a kasa:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng