Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa na bincike akan kisan jami’an yan sanda 7 da aka yi a Abuja
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi kira ga a binciki mutuwar yan sanda bakwai da aka rahoto cewa yan bindiga sun kashe a shataletalen Galadimawa, dake Abuja a ranar Litinin, 2 ga watan Yuli.
Shugaban majalisar dattawan ya bukaci shugaban kwamitin yan sanda na majalisar, Abu Ibrahim da ya yi duba cikin lamarin sannan ya dawowa majalisa da rahoto.
Saraki ya ce: “Ina so mu binciki lamarin dake kewaye da kisan jami’an yan sanda bakwai sannan kuma mu san ta yadda zamuyiwa iyalansu ta’aziyya. Don su san cewa mun damu sannan mun san abunda suke yi don tsaron rayukanmu.
KU KARANTA KUMA: Dattawan Bauchi sun sanya shugaba Buhari a gaba kan Dogara
“Don haka muna so dan Allah shugaban kwamitin yan sanda na majalisa kayi bincike akan lamarin sannan ka bamu rahoto a mako mai zuwa.”
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng