An bukaci gwamnatin Najeriya da ta zakulo masu haddasa kashe-kashe
Ana ta samun karin korafe-korafe ga gwamnatin Najeriya kan ta gudanar da bincike akan zargin da wani dan Majalisar wakilai ya yi na cewa an horas da wasu matasa 300 a wata kasa domin su dinga kashe jama’a.
An kuma bukaci gwamnatin Najeriya ta dauki mataki ko kuma matakan zakulo masu daukan nauyin masu karkashe mutane ya kara yawa, bayan wata sanarwar da dan majalisa Ahmed Idris Wase ya gabatar cewa, akwai wasu ‘yan siyasa dake haddasa da rikici, musamman tsakanin makiyaya da manoma.
Ahmed Idris Wase ya ce wannan ikirari yana kunshe cikin wani rahoton da suka baiwa gwamnatin Plateau. Ya ce suna da shedar cewa mutane fiye da dari uku aka tura kasar Israila, domin samun horo akan karkashe mutane.
Ya sha alwashin ba kakakin majalisa, Yakubu Dogara wannan rahoto. Ahmed Idris Wase ya ce akwai masakan makamai hudu da aka kai yankin arewa ta tsakiya aka zabawa ‘yan siyasa masu tada fitina.
Shugaban kungiyar Izala, Shaikh Abdullahi Lau ya nemi gwamnati ta binciki rahoton saboda tayiwa tufkar hanci. A cewarsa ya kamata a hukunta wadanda aka samu da hannu a lamarin. Idan ba haka aka yi ba, tamkar an ba kowa lisisin ya dauki doka a hannunsa ne.
KU KARANTA KUMA: Hukumar Soja ta karyata jita - jitar dake nuna cewar zasu dauki sabbin ma'aikata
Shi ma shugaban matasa na kungiyar Kiristoci reshen arewa mai bishara Musa Misal ya ce lallai baragurbin ‘yan siyasa na yin anfani da matasa, yana cewa shi dan siyasa idan yana neman kujera bai damu da wanda zai mutu ba muddin ya samu kujerar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng