Dattawan Bauchi sun sanya shugaba Buhari a gaba kan Dogara
Manyan shugabannin siyasa daga jihar Bauchi sun rubuta korafi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari gabannin zaben 2019, sunce lallai yayi aiki da dansu, kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.
A wata budaddiyar wasika da suka aikewa shugaban kasar, dattawan Bauchin sun roki Buhari da ya dauki mataki don magance sabanin siyasa tsakanin kungoyi daban daban a jihar su.
Wasu shugabanni da suka nuna goyon bayansu ga Dogara sune tsohon gwamnan jihar; Isa Yuguda, tsoffin ministoci uku, wato: Alhaji Muhammad Bello Kirfi, (Wazirin Bauchi), Muhammad Habib Aliyu (Tafidan Ningi), tsohon karamin ministan sufuri, da kuma Dr. Ibrahim Takubu Lame, (Santurakin Bauchi), tsohon ministan harkokin yan sanda.
Sanatocin da suka sanya hannu a wasikar sun hada da Sanata Suleman Nazif Gamawa, Bauchi ta Arewa; Isah Hamma Misau, Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa; Salisu Matori (Danmasanin Bauchi) da kuma Sanata Bala Adamu Kariya.
KU KARANTA KUMA: Allah da lokaci ne kadai za su iya kawo karshen APC amma ba sabuwar PDP ba - Ndume
Sannan kuma akwai tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Alhaji Muhammad Noma (Jarman Bauchi); Jakadan Najeria a kasar Jamus, Yusuf M. Tuggah da kuma Manjo Janar Yakubu Usman (mai ritaya).
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng