Nuhu Ribadu Ya Gano Yadda Ake Amfani da Kafafon Sada Zumunta wajen Haddasa Rikici a Najeriya

Nuhu Ribadu Ya Gano Yadda Ake Amfani da Kafafon Sada Zumunta wajen Haddasa Rikici a Najeriya

  • Nuhu Ribadu ya bayyana cewa ana amfani da kafofin sada zumunta wajen yaɗa labaran ƙarya da tayar da rikici tsakanin al’umma
  • Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya buƙaci a ƙarfafa hanyoyin gano barazanar tsaro tun da wuri gabanin zaɓen 2027
  • Ya ce ya kamata hukumomi su riƙa yin rigakafin matsalolin tsaro tare da bai wa kowa kariya daidai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce kafofin sada zumunta sun zama babbar matsala saboda ana amfani da su wajen yaɗa labaran ƙarya, ƙara gishiri da kuma haddasa rikici.

Ribadu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin taron ƙasa kan samar da tsaro a babban zaɓen 2027, wanda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya fadi abin da zai hana Arewa karbar mulkin Najeriya a 2027

Nuhu Ribadu.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

The Cable ta ruwaito Ribadu na cewa rikice-rikicen siyasa da suka shafi zaɓe da aka samu kwanan nan a wasu sassan ƙasar sun nuna muhimmancin yin shiri da wuri da kuma ɗaukar matakan hana faruwar matsaloli.

Ribadu ya hango matsalolin yan midiya

Ya bayyana cewa ƙaruwar tasirin kafofin sada zumunta da fasahar AI sun sauƙaƙa wa mutane yaɗa bayanan ƙarya da za su iya haddasa zaman doya da manja tsakanin al’ummomi.

Nuhu Ribadu ya ce:

“Wannan kafofin sada zumunta babbar matsala ce. Ana ƙirƙirar labaran ƙarya, ana ƙara gishiri, ana haddasa matsala tsakanin mutane. Mutum guda a ƙauye zai zauna ya aika da wani abu da zai haddasa rikici, sau da yawa ma ƙarya ce.
“Wannan ita ce rayuwar zamani da muke ciki yanzu. Ya kamata mu kasance masu lura da hakan. Dole ne mu ƙarfafa hanyoyin gano barazanar tsaro tun da wuri, mu tantance barazanar da ke tasowa, sannan mu magance wuraren da ka iya zama cibiyoyin rikici.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ayyana yaki da yan bindiga, ya ƙaddamar da dakarun tsaron daji 1,000

“Dole ne tsarinmu ya kasance na yin rigakafi tun da wuri, tare da bai wa kowa kariya daidai gwargwado."

Kiraye-kirayen sanya dokoki

Kalaman Ribadu sun zo ne a daidai lokacin da wasu jami’an gwamnati da ’yan majalisa ke kira da a samar da dokokin da za su kula da amfani da kafofin sada zumunta a Najeriya.

Nuhu Ribadu.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron Najeriya, Malam Nuhu Ribadu yana jawabi a wurin taro Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Twitter

A shekarar 2023, Hukumar Kula da Kafofin Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC) ta ce ta miƙa wa Majalisar Tarayya wani kudirin doka da ke neman samar da ƙa’idojin amfani da kafofin sada zumunta.

Hukumar ta nemi a soke tare da sake kafa dokar NBC, mai lamba CAP L11, ta dokokin Tarayyar Najeriya ta shekarar 2004.

Ribadu ya ce yan ta'adda sun canza salo

Kun ji cewa Nuhu Ribadu ya bayyana damuwarsa kan yadda ƙungiyoyin 'yan ta'adda ke ƙara dogaro da fasahohin zamani irin su AI, Kirifto, da jirage marasa matuka wajen kai hare-hare.

Ribadu ya jaddada cewa amfani da fasahohi irin su AI wajen ƙirƙirar saƙonnin yaudara da kuma amfani da Kirifto wajen gudanar da mu'amalar kuɗi ya ƙara sarƙaƙiya ga kalubalen tsaron a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262