Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shirin Tallafin Teloli a Najeriya, kowane Mutum Zai Iya Samun N5m
- Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin tallafa wa telolin a faɗin Najeriya, inda kowannensu zai samu tallafin Naira miliyan 5
- Bayanai sun nuna cewa shirin zai gudana na tsawon shekaru biyar ta hannun Asusun Horar da Masana’antu (ITF)
- Rahotanni sun nuna cewa an zaɓi teloli 150 daga yankin Arewa ta Tsakiya domin shiga matakin gwaji na shirin kafin ba su tallafin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shirin tallafa wa masu sana’ar ɗinki wadanda aka fi sani da teloli domin bunkasa kasuwancin su.
Shirin zai zakulo teloli 600 a faɗin Najeriya domin su amfan tallafin kuɗi da nufin bunƙasa kasuwancinsu har na Naira 5 kowannensu, amma za su biya kudin nan gaba.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa shiirin mai suna Business Incubation for Renewed Hope Tailors Programme zai gudana ne na tsawon shekaru biyar, kuma Asusun Horar da Masana’antu (ITF) ne zai aiwatar da shi.

Kara karanta wannan
Nuhu Ribadu ya gano yadda ake amfani da kafafon sada zumunta a haddasa rikici a Najeriya
An tsara shirin ne domin taimaka wa ƙwararrun masu sana’ar ɗinki su kafa sana’o’insu, ƙarfafa su da kuma faɗaɗa harkokinsu, tare da samar da guraben ayyukan yi a sassan ƙasar.
ITF ta sanar da shirin ne yayin wani taron wayar da kan jama’a gabanin ƙaddamar da shi a Jos, jihar Filato, inda ta bayyana cewa an zaɓi telo'o 150 daga yankin Arewa ta Tsakiya domin shiga matakin gwaji na shirin.
Shirin na daga cikin hanyoyin da ITF ke bi wajen taimaka wa waɗanda suka kammala shirin horas da masu sana’o’i mai suna Skill-Up Artisans Programme (SUPA) su samu damar bunƙasa sana’o’insu.
Waɗanda suka cancanci shirin
Shirin a buɗe yake ga waɗanda suka halarci shirin SUPA na ITF da kuma teloli waɗanda suka samu horo a wajen shirin.
Sai dai, ana buƙatar masu sha’awar cin gajiyar shirin su cika wasu ƙa’idoji kafin su cancanci shiga.
Yadda teloli za su nemi tallafin
ITF ba ta sanar da ranar rufe neman shiga shirin a faɗin ƙasar ba, haka kuma ba ta tabbatar da cewa ta buɗe sabon lokacin karɓar sababbin buƙatu daga telolin Najeriya ba.
Sai dai, ƙa’idojin da hukumar ta tanada na shirin bunƙasa sana’o’i sun nuna cewa ana iya yin rajista ta ofisoshin hukumar da ke yankuna daban-daban.
Masu sana’ar ɗinki da ke sha’awar shiga shirin za su iya zuwa ofishin ITF mafi kusa da su domin karɓar fom ɗin neman shiga shirin bunƙasa sana’o’i da kuma cikawa.
Haka kuma, za su iya ziyartar shafin hukumar na hukuma, www.itf.gov.ng, domin samun bayanai kan shirye-shiryenta da hanyoyin neman shiga.
Teloli, waɗanda ba su halarci shirin SUPA ba, dole ne su tabbatar sun mallaki takardar shaidar cancanta da lasisin da ITF ke buƙata domin cika ƙa’idojin shiga shirin.
Haka kuma, ƙa’idojin shirin bunƙasa sana’o’in ITF sun bayyana cewa shiga shirin kyauta ne, ba a biyan kuɗi.
Abin da ITF ta
Shugaban ITF, Dakta Afiz Oluwatoyin Ogun, wadda daraktar kula da harkokin shari’a, Safiya Abubakar, ta wakilta, ta ce shirin ya yi daidai da ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ta bayyana cewa ajandar na da manufar inganta ƙwarewar masu sana’o’in hannu a Najeriya domin su kai matakin ƙwarewa da ake buƙata a ƙasashen duniya.
A cewarta, shirin zai bai wa tela da aka zaɓa damar bunƙasa sana’o’insu bisa tsari, tun daga matakin farawa har zuwa lokacin da sana’ar za ta kai matsayin da ta manyanta cikin shekaru biyar.
Yadda za ka duba tallafin N100,000
Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda mutane za su gane idan suna cikin wadanda za a bai wa tallafin iyali na N100,000 a Najeriya.
Hukumar kula da shirin ta ce za a aika wa waɗanda suka yi nasara saƙonnin SMS domin sanar da su cewa an zaɓe su, tare da bayyana musu ƙarin matakan yadda za su karɓi kuɗin tallafin.
Asali: Legit.ng

