2019: Doyin Okube ya shawarci Saraki da ya tsaya takarar shugabancin kasa

2019: Doyin Okube ya shawarci Saraki da ya tsaya takarar shugabancin kasa

Wani babban jigon jam’iyyar Accord Party kuma kakakin tsohon shugaban kasa . Doyin Okupe, ya shawarci shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki da ya yi amfani da shaharrarsa a kasar ya nemi takarar shugabancin kasa a zaben 2019.

Okupe ya bayyana hakan ne ya yi da ya bayyana a matsayin bako a shirin Sunrise Daily, wani shirin kalaci da gidan talbijin din Channels ta gabatar a ranar Litinin, 9 ga watan Yuli.

A cewarsa Saraki na da gogewa da kwarewa a harkar siyasa, inda ya fara daga hadimin shugaban kasa, zuwa gwamna na zango biyu, sannan kuma a yanzu yana a matsayin shugaban majalisar dattawa.

2019: Doyin Okube ya shawarci Saraki da ya tsaya takarar shugabancin kasa

2019: Doyin Okube ya shawarci Saraki da ya tsaya takarar shugabancin kasa

Cewa ya hau matakai daban-daban na shugabanci saboda haka ya cancanci zama shugaban kasar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: An bukaci gwamnatin Najeriya da ta zakulo masu haddasa kashe-kashe

Okupe ya kara da cewa APC za su yi wa kansu alfarma ne idan har suka hana shugaban kasa Muhammadu Buhari takara a 2019, sannan kuma ya shawarci Saraki da ya bar jam’iyyar saboda masu masa bakin ciki na da yawa a jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel