Abun dariya ne danganta ni da Saraki ga fashin Offa – Gwamnan jihar Kwara

Abun dariya ne danganta ni da Saraki ga fashin Offa – Gwamnan jihar Kwara

Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed ya kuma sukar masu danganta shi da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ga lamarin fashin da yayi sanadiyan rasa rayuka a Offa.

Gwamnan yayi Allah wadai da lamarin a lokacin wata hira a gidan tyalbijin din Channels a wani shirin siyasa na musamman da ake nunawa a ranar Litinin.

“Abun dariya ne gani da jin cewa ni ko Saraki za mu kasance a abunda zai zamo halaka ga abun da muke zuba kudadenmu, don ganin rayuka da ayyukan mutane sun inganta,” inji shi.

Abun dariya ne danganta ni da Saraki ga fashin Offa – Gwamnan jihar Kwara
Abun dariya ne danganta ni da Saraki ga fashin Offa – Gwamnan jihar Kwara

Gwamna Ahmed yayi mamakin yadda za’a iya yin wannan zargi akan sa da shugaban majalisar dattawa, bayan sun shafe shekaru masu yawa don ganin sun aiki mai kyau tare da tabbatar da cewa dimokreadiyya ya isa ga mutane.

Ya soki lamarin da mutane ke kokarin ganin sunyi kazai mai girma ga manyan yan kasa a gidajen talbijin na kasa maimakon mayar da hankali kan yadda za’a magance ayyukan ta’addanci.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buratai ya mika mambobin kungiyar Boko Haram 184 ga majalisar dinkin duniya

Ya jaddada cewa lokaci yayi day a kamata a maida hankali sosai ga lamuran tattalin arziki da tsaro a kasar domin mutane su sa kwanciyar hankali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng