Da Gaske Baturiya Ta ba Iyalan Sarkin Daura Haƙuri? Ta Yi Bayani a Shafinta
- Mirka Cze ta yi martani kan rahotannin da ke cewa ta nemi afuwar Sarkin Daura, bayan zargin da ta yi masa na cin zarafinta a fadarsa
- Matar ta bayyana cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka nuna ta tana kuka tana neman afuwa, na bogi ne da aka ƙirƙira ta amfani da AI
- Ta ce duk da cin zarafi da saƙonnin barazana da take samu a shafinta na Instagram, ba za ta bari hakan ya karya mata gwiwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Daura, Katsina – Wata mata mai yawon buɗe ido daga ƙasar Poland, Mirka Cze, ta yi magana kan sabon bidiyon da ke yawo a kafafen sadarwa.
Cze ta fito ta karyata rahotannin da ke cewa ta nemi afuwar Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, kan zargin cin zarafinta da ta yi a fadarsa.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: An kai wa fitacciyar 'yar TikTok kuma 'yar Kwankwasiyya hari a Kano

Source: Facebook
A cikin wani saƙo da ta wallafa da PM News ta gano a ranar Juma'a, 27 ga watan Nuwamba, 2026, Cze ta bayyana cewa ba ta nemi afuwar Sarkin, iyalansa ko al'ummar Najeriya ba.
Baturiya ta karyata ba da hakuri
Ta ce bidiyon da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, wanda aka nuna ta tana kuka tana neman afuwar basaraken, an ƙirƙire shi ne ta hanyar amfani da fasahar AI domin yaudarar jama'a.
Cze ta ce:
"Ban nemi afuwar kowa ba. Bidiyon da ake yaɗawa an ƙirƙire shi ne ta amfani da AI. Abin mamaki ne, kuma wata hanya ce da aka shirya domin yaɗa bayanan ƙarya."
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a makon da ya gabata bayan matar ta wallafa wani bidiyo da ta ɗauka da tabarau mai fasahar zamani na Ray-Ban Meta.
A cikin bidiyon, ta zargi Sarkin Daura mai shekaru 92 da taɓa jikinta da ƙirjinta ba tare da izininta ba lokacin da ta kai masa ziyara a fadarsa.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Source: Original
Dalilin ta na zuwa fadar Sarkin Daura
A cewar bayanin da ta bayar a baya, ta ziyarci fadar ne a matsayin wani ɓangare na rangadin da take yi a Najeriya, inda aka ba ta damar ganawa da basaraken kafin faruwar abin da ta yi zargin cin zarafi ne.
Sai dai gwamnatin jihar Katsina ta dakatar da dukkan ayyukan hukuma da tafiye-tafiyen Sarkin a ranar 26 ga watan Nuwamba, yayin da ake gudanar da bincike kan zargin.
Gwamnatin ta kuma kafa kwamitin mutum tara ƙarƙashin jagorancin tsohon Alƙali Amiru Sanusi domin gudanar da bincike kan lamarin, cewar Daily Post.
A yayin da ake jiran sakamakon binciken, an sa ran babban mai ba Sarkin shawara, Galadiman Daura, zai kula da harkokin masarautar na ɗan lokaci.
Haka kuma, Cze ta wallafa hotunan wasu saƙonnin cin mutunci da ta ce ake aika mata ta shafinta na Instagram tun bayan barkewar rikicin.
Ta bayyana cewa duk da kalaman da take fuskanta suna ɓata mata rai, ba za su iya karya mata gwiwa ba.
Lamarin ya ci gaba da tayar da muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu ke kira da a gudanar da cikakken bincike kan zargin, yayin da wasu ke jan hankali kan yaɗa bidiyoyi da bayanan bogi da aka ƙirƙira ta hanyar fasahar zamani.
Kwamishinan Ganduje ya soki Sarkin Daura
An ji cewa tsohon kwamishinan harkokin addini a Kano, Dr. Tahir Baba Impossible, ya soki Sarkin Daura kan zargin da ake masa.
Baba Impossible ya bayyana cewa bai dace basarake mai daraja da martabar sarauta irin ta Sarkin Daura ya aikata hakan ba.
Malamin ya kuma yi kira ga malamai da su daina kare duk wanda ya aikata laifi, yana mai cewa babu bambanci tsakanin babba da ƙarami.
Asali: Legit.ng
