Ministan Tsaro Ya Ayyana kan Shi a Matsayin Cikakken Dan APC

Ministan Tsaro Ya Ayyana kan Shi a Matsayin Cikakken Dan APC

  • Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya kare halartar tarukan siyasar APC, yana mai cewa ya yi ritaya daga aikin soja
  • Musa ya ce duk da kasancewarsa dan APC, aikinsa na tabbatar da tsaro ya shafi dukkan jam'iyyun siyasa, ba jam'iyyar da yake ciki kadai ba
  • Ya kuma yi alkawarin cewa ma'aikatar tsaro za ta hada kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da zaben 2027 cikin gaskiya da adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ce yana da 'yancin shiga harkokin siyasar jam'iyyar APC saboda ya bar aikin soja.

Musa ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata hira, inda aka tambaye shi dalilin halartar tarukan yakin neman zaben APC da yadda yake bambance matsayinsa na dan siyasa da aikinsa na ministan tsaro.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Christopher Musa
Ministan tsaro, Christopher Musa. Hoto: GEN CG Musa
Source: Twitter

A bayanin da ya yi wa gidan talabijin na Arise TV, ya ce ba ya cikin aikin soja a yanzu, don haka yana da damar bayyana jam'iyyar da yake goyon baya.

Maganar ministan tsaro kan siyasa

Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya ya ce halartar tarukan siyasa na da nasaba da bukatarsa ta tabbatar da cewa jami'an tsaro suna gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Ya jaddada cewa wannan nauyi bai takaita ga APC ba, domin jami'an tsaro na da alhakin kare dukkan jam'iyyun siyasa.

Musa ya ce yana son ganin Najeriya ta zauna lafiya, kuma ba za su goyi bayan duk wani abu da zai haddasa tashin hankali ba.

Ya kara da cewa Shugaba Bola Tinubu ya sha umartar mambobin gwamnatinsa da kada su bari a gudanar da zabe cikin tashin hankali.

Maganar tsaro a zaben 2027

Musa ya ce ma'aikatar tsaro da rundunonin sojojin Najeriya za su hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki, ba tare da la'akari da jam'iyyar da suke ciki ba, domin tabbatar da zaben 2027 cikin gaskiya, adalci da sahihanci.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa ba zan goyi bayan Tinubu, Atiku ko Obi ba': Bulama Bukarti

Punch ta wallafa cewa ya ce burinsu shi ne kowane dan Najeriya ya samu damar fita ya kada kuri'arsa ga dan takarar da yake so ba tare da fargaba ba.

Christopher Musa
Janar Christopher Musa a wajen taro. Hoto: Defence HQ
Source: Facebook

Da aka tambaye shi yadda gwamnati za ta tabbatar wa jam'iyyun adawa da suka koka kan tashe-tashen hankula a lokacin siyasa cewa za a kare su, Musa ya ce rikice-rikice ba su takaita tsakanin jam'iyyun adawa da masu mulki ba.

Ya yi ikirarin cewa ana samun sabani da rikici a cikin jam'iyyun siyasa da kansu, musamman idan aka samu rashin jituwa kan wadanda za su tsaya takara ko sauya sunayen 'yan takara.

'Yan APC sun yi hadari

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya dage gangamin yakin neman zaben APC na shiyyar Kudancin Borno bayan wasu hadurran mota biyu da suka yi sanadin mutuwar mutane.

Hadurran sun faru ne a kan hanyoyin Biu zuwa Damaturu da Maiduguri zuwa Damboa, yayin da magoya bayan jam'iyyar ke tafiya Maiduguri domin halartar gangamin yakin neman zaben shugaban kasa.

Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Dauda Iliya, ya ce Zulum ya bayyana rasuwar mutanen a matsayin babban rashi ga masarautar Biu da jihar Borno baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng