Akwai Matsala: An Huro Wa Atiku Wuta kan Neman Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

Akwai Matsala: An Huro Wa Atiku Wuta kan Neman Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

  • CNDS ta yi gargadin cewa burin Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 na iya kawo cikas ga tsarin karba-karba
  • Ƙungiyar ta bukaci ’yan Najeriya su ƙi amincewa da takarar Atiku, tana mai cewa ya kamata Kudu ta kammala wa’adin shekaru takwas kafin mulki ya koma Arewa
  • CNDS ta ce mutunta tsarin rabon mulki na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ƙungiyar Concerned Nigerians for Democratic Sustainability (CNDS) ta yi gargadin kan takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2027.

Ta bayyana cewa burin Atiku na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 na iya kawo cikas ga tsarin karba-karbar mulki tsakanin Arewa da Kudu, tare da barazana ga haɗin kan Najeriya.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya fadi abin da zai hana Arewa karbar mulkin Najeriya a 2027

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a taron matasan ADC a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A rahoton Leadership, ƙungiyar ta bukaci ’yan Najeriya daga sassan ƙasar su juywa Atiku baya, tana mai cewa ya kamata Kudu ta kammala wa’adin shekaru takwas na shugabancin ƙasa kafin mulki ya koma Arewa a 2031.

Ana zargin takarar Atiku barazana ce

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Emeka Johnson, ya fitar, CNDS ta ce zaman lafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya tun daga shekarar 1999 ya ta’allaka ne, a wani ɓangare, kan fahimtar juna tsakanin Arewa da Kudu.

Johnson ya lura cewa Arewa ta yi shekaru takwas cikakku a kan karagar mulkin Najeriya ta hannun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, daga 2015 zuwa 2023.

Ya ce duk wani yunƙuri na katse wa’adin Kudu kafin ta kammala irin wannan zangon shekaru takwas ya saɓa wa yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma, kuma burin Atiku na 2027 shi ne irin wannan yunƙuri.

Ya ce:

“Abin da ke haɗa kan Najeriya shi ne amana, ba ƙarfi ba. Idan wani yanki ya yi shekaru takwas, adalci na buƙatar a bai wa ɗayan yankin shekaru takwas shi ma.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun raɗawa Atiku sabon suna gabanin zaben shugaban ƙasa na 2027

"Atiku na neman ’yan Najeriya su yi watsi da yarjejeniyar da ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiyar ƙasar nan, kawai saboda burinsa na kashin kai ba zai iya jira ba.”

Zargin Atiku da karya yarjejeniya

Johnson ya tuna cewa a 2024 ya rubuta wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa wasiƙa, inda ya ba da shawarar kafa tsarin shugabancin ƙasa na shekaru shida kacal, wanda za a riƙa musaya tsakanin Arewa da Kudu.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta ADC, Atiku Abubakar Hoto: @Atiku
Source: Facebook

Ya ce Atiku ya kuma yi alƙawarin mayar da tsarin karba-karba cikin kundin tsarin mulki idan aka zaɓe shi, amma duk da haka ya ƙi mutunta tsarin a aikace.

Ya ƙara da cewa shugabancin ƙasa mai mutane sama da miliyan 200 da ɗaruruwan ƙabilu na buƙatar mutum mai aiwatar da abin da yake da'awa da bakinsa.

Jigon PDP ya nemi Atiku ya janye

Kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Bode George, ya bukaci Atiku Abubakar ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027.

George ya ce bisa tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, ana sa ran kujerar shugaban ƙasa za ta koma Arewa a shekarar 2031, don haka Atiku zai iya sake neman takarar a lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262