Bayan Tara Malamai 2,000, Barau Jibrin Ya Haɗa kan Sarakuna 3,000 a Kano

Bayan Tara Malamai 2,000, Barau Jibrin Ya Haɗa kan Sarakuna 3,000 a Kano

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Jibrin Barau, ya tara sarakunan gargajiya 3,405 daga Kano ta Arewa
  • Barau ya bukaci dagatai, masu unguwanni da shugabannin kauyuka su yi amfani da matsayinsu wajen karfafa wa al’ummominsu gwiwar zaben ’yan takarar APC
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kuma bayyana cewa Kano za ta samu ayyukan wutar lantarki sama da Naira biliyan 130

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Jibrin Barau, ya kaddamar da sabon shirin neman goyon bayan siyasa, inda ya tara sarakunan gargajiya 3,405 a Kano.

Sarakunan sun fito ne daga Kano ta Arewa domin marawa Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran ’yan takarar APC baya a zaben 2027.

Barau ya tara sarakunan gargajiya
Sanata Barau Jibrin yayin taro da sarakunan gargajiya a Kano. Hoto: Barau I Jibrin.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, Barau ya yabawa sarakunan gargajiyar bisa gudummawarsu wajen ci gaban al'umma.

Kara karanta wannan

Makinde ya shirya marawa Atiku baya a zaɓen 2027? An samu bayanai

An gudanar da taron ne ranar Alhamis a cibiyar Ali Jita da ke Kano, inda aka samu halartar masu unguwanni 3,032, shugabannin kauyuka 347 da wakilai da sakatarorin hakimai 26.

Bukatar Barau Jibrin ga sarakunan gargajiya

Barau, wanda ke neman komawa majalisar dattawa a zaben 2027, ya bukaci sarakunan su yi amfani da tasirinsu wajen wayar da kan al'ummominsu domin zaben Tinubu, Gwamna Yusuf, shi da sauran ’yan takarar APC.

Wannan taro na daga cikin kokarin da mataimakin shugaban majalisar dattawan ke yi na tuntubar manyan masu fada a ji da kungiyoyi daban-daban a Kano ta Arewa yayin da APC ke shirin tunkarar zaben 2027.

Ya bayyana cibiyoyin sarautun gargajiya a matsayin muhimman abokan gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da walwalar jama'a.

Ya ce kusancin sarakunan da talakawa da kuma fahimtarsu kan matsalolin da al'ummomi ke fuskanta na sanya hadin kansu da gwamnati ya zama wajibi domin samun nasarar manufofin ci gaba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura wa Atiku saƙo bayan cika shekaru 80, ya tuna halaccin da ya yi masa

A cewarsa, wannan mataki zai taimaka wajen karfafa ayyukan tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Baya ga neman goyon bayan siyasa, Barau ya yi bayanin wasu manyan ayyukan gwamnatin tarayya da ake sa ran za su kawo sauyi a bangaren tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Kano ta Arewa.

Ya bayyana cewa ayyukan samar da wutar lantarki da aka shirya yi a Bichi, kasuwar Dawanau da Kwanar Kanye da ke karamar hukumar Kabo za su lashe sama da Naira biliyan 130.

Ya ce idan aka kammala ayyukan, za su bunkasa masana'antu da kasuwanci tare da samar da guraben ayyukan yi ga jama'a.

Barau ya ce:

"Mai yiwuwa wadannan ayyuka su dauki lokaci kafin kammalawa, amma babu shakka za su sauya tattalin arzikin mazabarmu ta dattawa."

Ya kuma tuna da irin tasirin ayyukan wutar lantarki da aka samar a jihar Ogun lokacin mulkin wani tsohon shugaban kasa, inda ya ce sun taimaka wajen mayar da jihar cibiyar masana'antu.

Tinubu zai yi nasara - Barau Jibrin

Kara karanta wannan

Barau Jibrin ya hada kan malaman Musulunci 2,000 saboda Tinubu, Abba Kabir

A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya ce duk alamu na nuna Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen 2027.

Barau ya yi wannan hasashen ne yayin ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓen APC a ƙananan hukumomi uku na Jihar Kano.

Ya buƙaci ’yan jam’iyyar APC su haɗa kai su yi aiki domin samun nasarar ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.