Zaben Gwamna: Mutumin Kwankwaso, Dantiye Ya Fadi Wanda Zai Zaba a Kano

Zaben Gwamna: Mutumin Kwankwaso, Dantiye Ya Fadi Wanda Zai Zaba a Kano

  • Baba Dantiye, MON, mni, FNGE ba zai goyi bayan takarar Aminu Abdussalam da Mustapha Rabiu Kwankwaso ba
  • Fitaccen ‘dan jaridar ya jero abubuwan da suka ja hankalinsa har ta sa zai sake goyon bayan Abba Kabit Yusuf a 2027
  • Dantiye na cikin kwamishinoni da aka tsige, amma wannan bai hana shi alkawarin ba APC kuri’arsa a takarar gwamna ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Baba Dantiye ya fito ya tabbatar da cewa a zaben gwamnan jihar Kano da za a yi a shekara mai zuwa, yana tare da jam’iyyar APC.

Baba Dantiye MON, mni ya shaida wa duniya cewa kuri’arsa tana wurin Abba Kabir Yusuf, matakin da watakila zai ba wasu Kanawa mamaki.

Abba Kabir Yusuf
Baba Dantiye da Abba Kabir Yusuf wajen kaddamar da motocin asibiti a Kano Hoto: Baba Dantiye/Hon. Salisu Muhammad Kosawa
Source: Facebook

Baba Dantiye ya fadi 'dan takaransa a Facebook

A wani dogon rubutu da ya yi a Facebook a yammacin Juma’a, kwararren ‘dan jaridar ya yi bayanin abin da ya sa zai bi bayan Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Fashola ya yi bayani kan zargin amfani da EFCC wajen tilasta wa gwamnoni komawa APC

Tsohon kwamishinan ya ce wani lokaci dole mutum ya ajiye son ran siyasa da hayaniya a gefe guda.

A rubutun, ya bada labarin yadda ya soma aikin gwamnati a matsayin malamin bincike tun lokacin Marigayi Abubakar Rimi yana gwamna.

Ya ce da Malam Ibrahim Shekarau ya zama gwamna a Kano, shi ya tura shi karo karatu a kasar Ingila, haka Rabiu Kwankwaso ya tafi da shi.

Bayan kasancewarsa sakataren yada labarai a 2011, ya rike Darekta Janar na harkokin yada labarai a lokacin gwamnatin Dr. Abdullahi Ganduje.

Aikin da Dantiye ya yi da Abba Kabir

Shi kuma Mai girma Abba Kabir Yusuf ya zabe shi ya zama Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida kafin ya tsige su a karshen 2024.

Duk da yadda ya rabu da Abba Kabir, Baba Dantiye zai ba gwamnan kuri’arsa, ba zai zabi jam’iyyar NDC da ta tsaida Aminu Abdussalam ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ce Abba Kabir na yunkurin sa EFCC ta bincike shi

Dattijon ya kawo ayyukan da ya yi da shugabanni dabam-dabam ne saboda ya nuna irin damammaki da ya samu a gwamnatin Kano na shekaru.

Meyasa Dantiye yake tare da Abba?

Dantiye ya ce ba wai yana goyon bayan gwamna Abba ba ne saboda sun fito daga yanki kusan guda; Karamar hukumar Gwale da ta birnin Kano (KMC)

Sai dai, ya ce yana tare da gwamnan a zaben 2027 ne ganin irin nasarorin da ya samu da kuma ayyukan da ya dauko da ba zai iya karasa su yanzu ba.

Ya kawo misali da ayyukan tituna da ake yi, ya bayyana yin hanyoyi a matsayin ma’aunin cigaba domin suna saukaka kasuwanci, sufuri da sauran harkoki.

Dantiye ya ce wannan gwamnati ta yi aikin hanyoyi da-dama a Fagge, Nassarawa, Tarauni, Gwale da Dala, bayan haka kuma ya ce an shiga cikin kauyuka.

Abba ya tado da kwangilar tituna a Gezawa, Albasu, Gwarzo, Dawakin Tofa, Tofa, Rogo, Sumaila, Dawakin Kudu, Ajingi da Rano daga 2023 zuwa yau.

Amma duk da wadannan ayyuka, Dantiye ya yarda cewa har yanzu akwai sauran ayyuka gaban Abba.

Kara karanta wannan

Ana fada wajen tallar Tinubu, jam’iyyar APC ta fito ta yi wa Wike wankin babban bargo

Wata hujja da ya kawo kuma ita ce gyaran makarantu da gina sababbin aji da kuma daukar malamai rututu tare da biyan kudin jarrabawar daliban sakandare.

Idan aka koma fannin kiwon lafiya, ‘dan jaridar ya ce gwamnatin APC tana da abubuwan nunawa.

A cewarsa, an gyara manyan asibitoci a Kumbotso da Rogo kuma an daga kimar asibitocin Garko, Garun Malam, Ghari, Shanono, Gabasawa da Rimin Gado.

Sauran nasarorin da gwamnatin Abba ta samu

Kamar yadda aka dauki malamai, an dauki ma’aikatan lafiya 2, 037 aiki ban da kananan motocin kai afajin gaggawa 484 da aka raba a duka mazabun Kano.

Domin ganin an tabbatar da tsaro, ya fake da jami’an Neighbourhood Watch Corps 2, 000 da aka dauka kuma aka raba masu motoci da babura su yi aiki.

Kokarin Barrister Muhuyi Magaji Rimingado wajen yaki da miyagun kwayoyi da fadan dab ana cikin abubuwan da suka ba APC kuri’ar Dantiye a 2027.

A bangarorin fansho da samar da ruwa, ‘dan jaridar ya ce Abba yana kokari duk da har yanzu akwai tsofaffin ma’aikatan da ba a biya su hakkokinsu ba.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Duba da wadannan, ya ce zai bada kuri’arsa ga Mai girma Abba idan lokacin zabe ya yi a Kano.

Rubutun ya kawo shawarwari na bangarorin da ya kamata gwamnati ta maida hankali a kansu kuma ta kara kokari domin Kanawa su amfana da mulki.

Yadda aka tsige Dantiye da wasu kwamishinoni

An ji labarin lokacin da Abba Kabir Yusuf Ibrahim ya kori Baba Dantiye, Ladidi Garko, Shehu Yammedi da Abbas Sani-Abbas daga kan kujerunsu.

Idan za a tuna, sannan ne Aminu Abdulssalam ya bar ma’aikatar raya masarautu, shi kuma Yusuf Ibrahim K/Mata ya koma kwamishinan kimiyya da fasaha.

Wannan sauyi ne ya taba Sakataren gwamnatin jihar Kano da ofishin shugaban ma'aikatan fadar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng