Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wadanda suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Laraba sun ce sun je ne domin bashi tabbacin goyon bayansu. Sun kuma sanar da shi cewar APC ce mai rinjaye.
Wasu da ake zargin yan fashi ne a ranar Talata sun kashe akalla mutane 20 a wani hari da aka kai kauyen Kwaddi dake karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara. A makon da ya gabata, kimanin mutane 30 aka kashe a wani hari irin wannan.
Alhaji Muhammad Bello Butu-butu, shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, ya karyata rade-radin dake yawo na cewa wasu mambobin jam'iyyar APC na majalisar dokokin jihar sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Gwamna Mohammed Bindow na jihar Adamawa yayi alkawarin bayar da Adamawa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019. Bindow ya bayana hakan ne a wani gangamin siyasa da jam’iyyar APC babin jihar Adamawa ta shirya masa.
Gwamnan jihar Ekiti mai jiran gado, Dr Kayode Fayemi yace da nasarar da yayi a ranar 14 ga watan Yuli, 2018, shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Kwamrad Adams Oshiomhole zai sake nasara a zaben jihar Osun mai zuwa da kuma zaben 2019
Majalisar dokokin jihar Adamawa, a ranar Litinin ta ce bata da labara kan zargin sauya shekar wasu yan majalisa daga APC, zuwa PDP. Shugaban kwamitin bayanai na majalisar, Alhaji Abubakar Isa yace mutun guda ce ta sanar da sauya
Fitaccen malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi kira ga yan siyasa akan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya bukaci yan siyasa nagari da su hada kai da shugaban kasar domin cigaban kasar.
Rundunar sojin Najeriya sun kaddamar da wani aikin tsaro na hadin gwiwa domin kakkabe yan ta’adda masu fashi a kauyukan Gandi da Tabanni dake karamar hukumar Rabbah na jihar Sokoto. Wannan aiki ya biyo bayan harin yan fashin.
Wani mamba a majalisar wakilai, Mansur Ali Mashi, ya bayyana cewa kiraye-kiraye na bayan nan da akeyi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus saboda rashin tsaro baida fa’ida. Mashi ya ce gadon matsalar Buhari yayi.
Aisha Musa
Samu kari