Gwamnatin Tinubu Ta Yi Maganar da Ta ba da Mamaki kan Tsaro
- Fadar shugaban kasa ta ce Najeriya ba ta karkashin hannun 'yan ta'adda kamar yadda 'yan jam'iyyun adawa ke fada a kwanan nan
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce hare-hare da garkuwa da mutane suna faruwa ne a wasu wurare a kasar
- Onanuga ya kara da cewa duk da korafin da ake yi, ‘yan Najeriya da dama na ci gaba da tafiye-tafiye zuwa jihohin kasar cikin aminci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta jaddada cewa Najeriya ba ta cikin wani hali na ƙunci ko mamaya duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.
Bayo Onanuga ya ce rahotannin rashin tsaro na haifar da tunanin cewa duk faɗin ƙasar ba ta da tsaro, yana mai jaddada cewa hare-hare da ayyukan ta’addanci suna faruwa ne a wasu takamaiman wurare kaɗai.

Source: Twitter
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise a ranar Talata.
Bayo Onanuga ya kore karfin matsalar tsaro
A cewar Onanuga, ‘yan Najeriya da dama na ci gaba da yin tafiye-tafiye a sassan ƙasar ba tare da fuskantar wata barazanar tsaro ba.
Ya kawo misalai daga tafiye-tafiyensa ta kan titi a cikin ƙasar, tare da ambaton wasu ‘yan Najeriya da ke yawan yin dogayen tafiye-tafiye.
Hadimin shugaban ƙasar ya kuma ambaci shugaban NELFUND, wanda a cewarsa ya sanar da shi kwanan nan cewa ya yi tafiya a mota daga Abuja zuwa jihar Kebbi.
Kiran Onanuga ga 'yan Najeriya
Onanuga ya buƙaci ‘yan Najeriya da kada su ɗauka cewa duk ƙasar na cikin ƙunci saboda rahotannin hare-hare da garkuwa da mutane.
Ya ce:
“Na yi tafiya daga Legas zuwa Oyo domin halartar jana’iza... Matsalar Najeriya ita ce kafafen yaɗa labarai ma suna ƙara haifar da matsaloli. Yadda suke ba da rahoton rashin tsaro kamar dai duk ƙasar ta faɗa cikin rikici.”
“Kada ku bari mutane su tsoratar da ku cewa duk ƙasar na cikin ƙunci. Ba haka ba ne. Abin da ake samu shi ne matsalolin tsaro a wasu wurare.
“Duk lokacin da na karanta labarin sace mutane ko wani hari a wani wuri, wani lokaci nakan duba lokacin da abin ya faru. Sai in ga ya faru da ƙarfe 8:00 na dare, ko 9:00 na dare, wani lokaci ma da ƙarfe 1:00 na dare.

Source: Facebook
Dauda Rarara ya yi magana kan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa mawakin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya caccaki masu yawan magana kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.
Rarara ya soki mawaki Davido game da sanya riga mai dauke da sunayen dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a wata makaranta a Oyo.
A wani bidiyo da ya fitar a makon da ya wuce, Dauda Rarara ya ce abin da Davido ya yi a kasar Amurka tona asirin Najeriya ne kuma bai dace ba.
Asali: Legit.ng

