2019: Bindow ya sha alwashin kawowa Buhari Adamawa
Gwamna Mohammed Bindow na jihar Adamawa yayi alkawarin kawowa shugaban kasa Muhammadu Buhari jiharsa a zaben 2019.
Bindow ya bayana hakan ne a wani gangamin siyasa da jam’iyyar APC babin jihar Adamawa ta shirya domin yi masa maraba da dawowa jihar a ranara Talata, 24 ga watan Yuli a Yola, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa kwarya-kwaryan walimar ya kasance domin nuna irin soyayyar da mutanen jihar ke yi masa, Buhari da kuma jam’iyyar.
Ya bayyana cewa taron da yadda jama’a suka hallara ya nuna cewa gwamnatin na yiwa mutanen hidima sosai.
KU KARANTA KUMA: Yayinda yan majalisa da yawa suka sauya sheka a APC, gwamnoni sun yunkura domin ceto jam’iyyar
“Da abunda idanuna ya gani a yau, na yarda cewa APC ce jam’iyyar dake da Adamawa,” inji gwamnan.
Ya kuma bayyana cewa Buhari zai lashe Adamawa da kuri’u mafi yawa saboda yadda ya kawo ci gaba a fadin kasar.
Ya roki mabiya da su tabbatar jam’iyyar APC ta yi nasara a dukkan matakai a zabe mai zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng