Mutane 20 sun mutu a harin masallaci da aka kai kauyen Zamfara
Wasu da ake zargin yan fashi ne a ranar Talata sun kashe akalla mutane 20 a wani hari da aka kai kauyen Kwaddi dake karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara.
A makon da ya gabata, kimanin mutane 30 aka kashe a wani hari makamancin wannan da aka kai kauuka biyar a yankin Gidan Gona dake karamar hukumar Maradun na jihar.
Kauyen Kwaddi wadda ke cikin kursugumin dajin sannan yake kewaye da duwtsu na iyaka da jumhuriyar Nijar yayinda mazauna yankin kan tsallake iyalar zuwa kasashen dake makwabtaka domin kasuwaci da sauran lamura.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mazauna yankin sunce yan bindigan sun kai farmaki kauyen da farko suka kashe akalla mutane takwas bayan sun gaza bayar da kudin fansar naira miliyan 1 daga mutanen garin.
KU KARANTA KUMA: Ministoci da Ma’aikatu sun dawo da Biliyan 118 cikin asusun Gwamnati
“Sun ba da lokacin da za’a biya kudin fansar sannan suka tafi. Yawancin mazauna garin manoma ne sannan babu wanda zai iya hada N50,000 a cikinsu. Sun dawo suka sake kai hari lokacin da mutane ke sallar Asr.
“Ana rowan sama a lokacin, sai suka bar masallacin sannan suka fara bin gida-gida suna kashe mutane a gidajensu ciki harda wadanda suka tsere zuwa masallaci,” cewar wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.
Kakakin yan sandan jihar, Muhammad Shehu ya tabbatar da lamarin amma ya ce ba zai iya ci gaba da bayar da wasu bayanai ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng