Babu dan majalisa daga APC da ya koma PDP – Majalisar dokokin Kano ta yi watsi da jita-jita

Babu dan majalisa daga APC da ya koma PDP – Majalisar dokokin Kano ta yi watsi da jita-jita

Alhaji Muhammad Bello Butu-butu , shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, ya karyata rade-radin dake yawo na cewa wasu mambobin APC na majalisar dokokin jihar sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

An rahoto cewa But-butu ya bayyana hakan ne a yayinda yake zantawa da manema Labarai a garin Kano a ranar Talata, 24 ga watan Yuli.

Ya ce jita-jitan baida tushe, kawai bita da kullin magauta ne dake kokarin ganin sun haddasa rudani a jihar.

Ya kara da cewa duk da cewar mambobin jam’iyyar shida sun kasance masu biyayya ga tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso amma har yanzu suna APC.

Babu dan majalisa daga APC da ya koma PDP – Majalisar dokokin Kano ta yi watsi da jita-jita

Babu dan majalisa daga APC da ya koma PDP – Majalisar dokokin Kano ta yi watsi da jita-jita

Ya kuma shawarci mutanen jihar da suyi watsi da labaran da wasu makirai ke yadawa a shafukan watsa labarai domin tada zaune tsaye a jihar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata,ya ce sauya shekar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) abune da ya kwana biyu.

KU KARANTA KUMA: Oshiomhole zai tabbatar da nasarar Buhari a 2019: Fayemi

Alhaji Ata ya tabbatar da cewar sauya shekar tashi ba zai shafi jam'iyyar APC ba, sannan kuma ba zai hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje maye kujerar shi ba a karo na biyu a zabe mai gabatowa na shekarar 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel