Harin Sokoto: Rundunar soji sun fara aiki na musamman
Rundunar sojin Najeriya sun kaddamar da wani aikin tsaro na hadin gwiwa domin kakkabe yan ta’adda masu fashi a kauyukan Gandi da Tabanni dake karamar hukumar Rabbah na jihar Sokoto.
A wata sanarwa da aka gabatar ga kamfanin dillancin labaran Naeriya a ranar Juma’a a Sokoto dauke da sa hannun kakakin sashi na 1, na rundunar sojin Sokoto, Clement Abiade, yace wannan aiki ya biyo bayan harin da yan fashin suka gudanar a ranar 9 ga watan Yuli wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Aikin ya hada da rundunar soji, sojin sama, yan sanda, NSCDC da kuma DSS sun fara a ranar Alhamis sannan kuma hakan zai kai har Zamfara.
KU KARANTA KUMA: Abunda muka tattauna da shugaba Buhari – Yan majalisa na APC
Kwamandan sashin, Kennedy Udeagbala, ya fadama dakarun das u tabbatar da an aiwaatar da aikin cikin hadin kai, da kuma kwarewa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng