An kori masu tsintar bola daga babban birnin tarayya Abuja
Hukumar raya babban birnin tarayya, Abuja ta hanawa masu tsintar bola bi kan titinan birnin su na tsintar shara a kwandunan sharar kofar gidaje.
A wata sanarwa daga jami’in yada labaran Ministan Abuja, Abubakar Sani ya ce hakan ya biyo bayan korafe-korafen rahotannin sace-sace da ake zargin masu kwasar bolar na yiwa jama’a.
Sanarwar ta ce ana zargin su da aiwatar da kananan sace-sace, fashi da makami da sauran kananan laifukan da ba za a ci gaba da kauwar da kai a kan su ba.
Sakatariyar Hukumar Tsaftace birnin, Ladi Hassan, ta kara da cewa matasan da da aka fi sa Baban Bola, su na kuma yawan satar kayan gwamnati a wurare da dama, sannan kuma akwai su da kauda ajiyar da ba su ne suka yi ba.
Daga nan ta shaida cewa an amince su yi harkokin Baban Bola a garuruwan Gousa, Karshi, Bwari, Gwagwalada, Kwali, Abaji da Kuje.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na halarci taron sanatocin APC da shugaba Buhari – Shehu Sani
A karshe ta yi kira ga jami’an tsaro su kama tare da gurfanar da duk wanda suka kama ya na tsintar bola a cikin birnin Abuja.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng