Abun dariya ne APC bata so Dogara ya bar jam’iyyar – Yan majalisar wakilai
Wasu mambobin majalisar wakilai a ranar Lahadi, sun bayyana yunkurin da jam’iyyar All Progressives Congress ke yi na hana kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party ko wata jam’iyya a matsayin abun dariya.
Yan majalisan sunyi Magana a karkashin lemar kungiyar damokradiyya na majalisa, wadda mai akasarinsu mambobin PDP da mambobin sauran jam’iyyun adawa.
Sun yi Magana bayan ganawarsu a Abuja. Sun nuna mamakin cewa APC ta fara yabama darajar Dogara bayan sauya shekar da yan majalisun dokokin kasar suka yi a makon da ya gabata.
A wata sanarwa daga kakakinta, Mista Timothy Golu, kungiyar ta shawarci APC da kada su bata lokacinsu domin kakakin majalisar zai bar jam’iyyar a duk lokacin da yayi masa.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa Dogara zai ci gaba da kasance kakakin majalisar domin APC kadai ba ita ke da masu rinjaye a majalisa da za su tsige shi ba.
KU KARANTA KUMA: Wasu manyan Sanatocin Arewa sun koka game da rikicin Zamfara
Kungiyar sun kuma bukaci Dogara da ya share APC ya saya shekarsa zuwa kowace jam’iyya.
A halin da ake ciki, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole na kokarin ganin ya sasanta masu hanzuga a jam’iyyar da suke ganin an maida su saniyar ware tun bayan zabarsa a matsayin shugaba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng