Kiraye-kiraye da akeyi na cewa Buhari yayi murabus baida fa’ida – Mashi
Wani mamba a majalisar wakilai, Mansur Ali Mashi, ya bayyana cewa kiraye-kiraye na bayan nan da akeyi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus saboda rashin tsaro baida fa’ida.
Mashi ya bayyana cewa matsalolin rashin tsaro abune da gwamnatin Buhari ta gada, ya kara da cewa tunda ya karbi mulki, lamarin ya ragu sosai.
Mashi ya bayyana cewa gwamnatin APC ta sadaukar da albarkatu da dama da karfi domin kare Najeriya. “Ya zama dole mutane du gode sannan su kwatanta da lokutan baya.”
A jiya shugabannin yanki sun bukaci shugaban kasa Buhari day a magance matsalolin da ake ciki na kashe-kashe ko kuma yayi murabus.
Yace maimakon yin Magana da kafafen watsa labarai kamata yayi su ziyarci Buhari su bayyana ra’ayinsu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng