Kannywood: Jaruma Zainab Indomie ta farka domin cigaba daga inda ta tsaya
Shahararriyar jarumar Kannywood Zainab Abdullahi wacca aka fi sani da Zainab Indomie na shirin dawo da sunanta a masana’antar.
An daina jin duriyar Indomie a masana’antar na tsawon wani lokaci bisa ga wasu dalilai.
Ubangidanta Adam Zango ne ya sanar da dawowar jarumar a shafinsa na Instagram.
Ya wallafa hotunanta saboda nuna farin cikin sa bisa biyayar da take nuna masa.
Jarumar tana daya daga cikin jarumai mata dake kan gaba da farfajiyar kamfanin White house family wanda Adam Zango ke jagoranta.
KU KARANTA KUMA: Masu sauya sheka na adawa ne da gwamnoni ba wai Buhari ba – Fadar shugaban kasa
Zainab Indomie tana daya daga fitattun matan kannywood da suka raya masana'antar gabanin fitowar sabbin fuskoki da ake damawa dasu yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng