An gurfanar da jami’in dan sanda tare da wasu mutane 9 akan kashe-kashen Plateau
An kama wani jami’in dan sanda a Barkin Ladi, jihar Plateau, kan zargi saida makamai ga barayin shan da sauran masu laifi.
An kama sajan Zakariah John yana siyarda makamai na musamman ga wani da ake zargin dan fashi ne.
Mafi akasarin hare-hare da kashe-kashe sa aka gudanar a Barkin Ladi, Riyom, Mangu da Bassa suna da nasaba da kananan makamai.
Jami’i labarai na Operatin Safe Heaven Manjo Adam Umar, wadda ya gurfanar da masu laifin a jiya ya ce: “Mun kama wani jami’in dan sanda Sajan Zakariah John, da wani mai fashi, Sani Muhammad dukkans sun kasance masu amfani da bindiga.
KU KARANTA KUMA: Masu sauya sheka na adawa ne da gwamnoni ba wai Buhari ba – Fadar shugaban kasa
"Haka kuma mun kama Patrick Choji da Yakubu Davou dauke da makamai ba bisa ka’ida ba. Dukka dai muna da masu laifi 10 wadanda sun aikata laifuka ne daban-daban kama daga fashi shau, fashi da makami, sojan gonad a mallakar bindigogi."
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng