Ya kamata yan siyasa nagari su ba Buhari hadin kai domin cigaban kasar – Sheikh Sani Yahaya Jingir

Ya kamata yan siyasa nagari su ba Buhari hadin kai domin cigaban kasar – Sheikh Sani Yahaya Jingir

Fitaccen malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi kira ga yan siyasa akan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya bukaci yan siyasa nagari das u hada kai da fata tare da shugaban kasar domin kawo ci gaba da ayyuka nagari a kasar.

Shehu malamin ya bukaci al’umman musulmi da su dage da addu’a domin ganin abubuwa sun daidaita a kasar.

KU KARANTA KUMA: Attahiru Jega ya fallasa babbar matsalar 'yan siyasar Najeriya Attahiru Jega ya fallasa babbar matsalar 'yan siyasar Najeriya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rundunar sojin sama dake gudanar da aikin operation lafiya dole, a ranar 15 ga watan Yuli sunyi nasarar kakkabe yan ta’addan Boko Haram da dama a Bulagalaye da Kwakwa, duk a jihar Borno.

Dukkanin nasarar da aka samu a wuraren biyu ya kasance sakamakon kokarin bin sahun yan ta’addan da sojin Najeriya ke yi bayan sun dakile harinsu a kusa da Bama.

A lokacin da suka samu rahoton harin sai sashin kwararru da jirgin yaki suka bazama don gano yan ta’addan dake tserewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel