An Yi wa Mutanen Sunday Igboho Jina Jina da Suka Gwabza da 'Yan Bindiga
- Rahotanni da suka fito daga Oyo sun nuna cewa an jikkata wasu jami'an sa-kai da ke da alaka da Sunday Igboho da suka je fafatawa da 'yan bindiga
- Tawagar tsaron Iru Ekun da ke da alaka da Igboho na gudanar da sintiri a daji ne domin gano maboyar masu garkuwa da mutane da sauransu
- Duk da yadda labarin ya bazu, zuwa yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka ji rauni ba kuma 'yan sandan jihar Oyo ba su fitar da sanarwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Rahotanni sun ce an jikkata wasu jami'an wata kungiyar tsaro mai zaman kanta da ke da alaka da mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho.
Hakan ta faru ne bayan da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne masu tsallaka iyakoki suka yi musu kwanton-bauna a yankin dajin jihar Oyo.

Source: Getty Images
Vanguard ta ce lamarin ya faru ne yayin da jami'an kungiyar tsaron Iru Ekun ke gudanar da wani samame domin gano masu garkuwa da mutane da sauran masu dauke da makamai da ake zargin suna boye a cikin babban dajin.
An jikkata mutanen Sunday Igboho
Majiyoyin da suka san yadda aikin ya gudana sun ce jami'an tsaron sun yi amfani da jirage marasa matuka domin gano maboyar wadanda ake zargi da kuma bibiyar motsinsu kafin su kutsa cikin yankin.
Sai dai an ce aikin ya rikide zuwa musayar wuta bayan da wasu mutane dauke da manyan makamai, wadanda ake kyautata zaton suna cikin kungiyoyin masu aikata laifuffuka masu tsallaka iyakoki, suka kai musu hari.
Sahara Reporters ta ce wadanda ake zargin 'yan bindigan ne suka fara bude wuta kan jami'an tsaron da ke ci gaba da kutsawa cikin dajin, lamarin da ya haddasa kazamin fada tsakanin bangarorin biyu.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin jami'an kungiyar Iru Ekun sun samu raunukan harbin bindiga a yayin musayar wutar, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a tabbatar da adadin wadanda suka jikkata ba.

Source: Original
'Yan sanda ba su yi magana ba
Kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar Oyo bai yi nasara ba, domin ba a samu kakakin rundunar, DSP Olayinka Ayanlade, ta wayar tarho ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Lamarin ya sake tayar da hankalin jama'a game da yawaitar ayyukan masu garkuwa da mutane, 'yan bindiga da sauran masu dauke da makamai da ke fakewa a dazuka da yankunan karkara a wasu sassan Kudu maso Yammacin Najeriya.
An kama kayan sojoji a Legas
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane uku dauke da kayan sojoji a cikin wata babbar mota.
Yayin da ake bincike, an gano buhuna kusan 50 cike da kayan sojoji da ake zargin za a mika su ga masu aikata laifi ne a Kudancin kasar.
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa za ta cigaba da kokari wajen kare rayuka da dukiyar 'yan kasa, inda ta nemi hadin kan al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

