Trump Ya Burma Matsala, Manyan Alkalan ICC Sun Kai Shi Kara Kotu
- Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugaban kasa, Donald Trump, ta kakaba takunkumi kan wasu alkalan kotun ICC
- Alkalan sun koka kan takunkumin da aka sanya masu inda daga karshe suka dauki matakin kai Donald Trump kara gaban kotu
- Takunkumin dai dai aka sanyawa alkalan ya biyo bayan sammacin da kotun ta bayar ne na cafke Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Manhattan, Amurka - Wasu alƙalan kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa (ICC) guda uku sun shigar da kara kan shugaban kasar Amurka, Donald Trump da gwamnatinsa.
Alkalan sun shigar da Shugaba Trump kara ne kan takunkumin da aka saka musu a shekarar da ta gabata, inda suka nuna cewa matakan sun kasance wadanda suka sabawa doka.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa an shigar da karar ne a babbar kotun tarayya da ke Manhattan ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026.
Alkalai sun kai karar Trump
Alƙalan Kimberly Prost ta ƙasar Canada, Solomy Balungi Bossa ta ƙasar Uganda, da Reine Adelaide Sophie Alapini-Gansou ta ƙasar Benin, sun bayyana cewa an tsara takunkumin ne domin matsin lamba da nufin azabtarwa da kuma tilasta masu.
Gwamnatin Trump ta saka takunkumi ne akan wasu alƙalai da dama a kotun ICC a shekarar da ta gabata a sakamakon fitar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kotun ta yi.
Sakamakon wadannan takunkumai, alƙalan sun fuskanci hana su amfani da kadarorinsu da kudaden da suke da su a Amurka.
Haka kuma, an hana hukumomi da ke Amurka gudanar da kowace irin harka ta kasuwanci ko mu'amala da su, ciki har da "samar da kuɗaɗe, kaya, ko ayyuka".
Wane aiki kotun ICC ke yi?
Kotun ICC, wadda aka kafa a shekarar 2002, tana da ikon shari'a na ƙasa da ƙasa domin gurfanar da masu laifin kisan kare dangi, laifuffuka take hakkin dan Adam kuma laifuffukan yaƙi a ƙasashen mambobi ko kuma idan kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tura mata lamarin.
Ko da yake kotun ICC tana da ikon shari'a a kan laifuffukan yaƙi, laifuffuka take hakkin ɗan adam, da kisan kare dangi a ƙasashe mambobinta guda 125, wasu ƙasashe, da suka haɗa da Amurka, China, Russia, da kuma Isra'ila, ba su amince da ikonta ba.
A lokacin mulkin farko na Trump, gwamnatinsa ta saka takunkumi a kan babbar mai shigar da ƙara ta kotun ICC ta wancan lokacin, Fatou Bensouda, da ɗaya daga cikin mataimakanta sakamakon aikin da kotun ke gudanarwa a kan Afghanistan.

Source: Facebook
Alkalai sun ce an saba doka
Ƙarar ta bayyana cewa takunkumin ya saɓa wa doka tun da ya wuce iyakar ikon da dokar IEEPA ta bayar, kuma ba a sanya su ne shi bisa wata barazana ta gaggawa ba, tashar New York Times ta kawo rahoton.
Alƙalan sun kuma ƙara da cewa takunkumin yana hana miƙa shaidu da hujjoji a kowace irin shari'a da ke jiran hukunci a gabansu.
Trump ya yi barazana ga Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kai hari a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaba Trump ya yi barazanar ne kan kasar Iran idan har ba ta dakatar da ƙungiyar Hezbollah daga “janyo matsala” ba.
Trump ya yi barazanar ne yayin da wakilan gwamnatin Amurka da Iran ke tattaunawa a kasar Switzerland da ke nahiyar Turai.
Asali: Legit.ng