Yanzu Yanzu: Allah yayiwa tsohon gwamnan Gombe, Hashidu rasuwa
Allah yayiwa tsohon gwamnan jihar Gombe, Abubakar Hashidu rasuwa.
Wata majiya tace Hashidu ya rasu a safiyar ranar Juma’a, 27 ga watan Yuli a gidansa dake Gombe bayan fya yi ama da rashin lafiya na tsawon wasu shekaru.
Ya kuma rasu yana da shekaru 74 a duniya.
Marigayi Hashidu ya yi gwamnan jihar Gombe daga watan Mayu 1999 zuwa watan Mayu 2003. An zabe shi a karkashin lemar jam’iyyar All Peoples Party (APP).
Wani makusancin iyalan marigayin ya tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan kuma za’a binne shi da karfe 5pm na yammacin yau Juma’a.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An saki Dino Melaye bayan anyi garkuwa da shi
Marigayin ya kuma rike mukamin ministan ruwa da kuma minitan gona da ci gaban karkara a lokacin mulkin Ibrahim Babangida.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng