Abunda muka tattauna tare da Buhari – Sanatocin APC

Abunda muka tattauna tare da Buhari – Sanatocin APC

Sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wadanda suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Laraba sun ce sun je ne domin bashi tabbacin goyon bayansu.

Sun bayyana cewa sun kuma sanar das hi cewar APC ce keda masu rinjaye a majalisun dokokin kasar har yanzu.

Ganawar wanda aka fara da misalin karfe 9:30pm a ofishin uwargidan shugaban kasa dake fadar shugaban kasa, Abuja.

Abunda muka tattauna tare da Buhari – Sanatocin APC
Abunda muka tattauna tare da Buhari – Sanatocin APC

Sanatoci 39 ne suka halarci taron, tare da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adam Oshiomhole da kuma manyan jami’an gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Ku dawo gida – PDP ga sauran tsoffin ‘ya’yanta bayan sauya shekar Ortom

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce yiwuwar sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na da karfi sosai.

Ibrahim A cewar jaridar Daily Trust, shugaban majalisar dattawan ya fadi hakan ne ga Reuters a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli. Furucin Saraki na zuwa ne yan kwanaki bayan sanatocin APC 14 sun bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP da ADC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng