Abin da ya sa ba zan rage farashin siminti ba – Dangote
Shahararren attajirin nan na Najeriya kuma mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilan da suka sanya ba zai iya karya farashin siminti ba, kamar yadda gwanatin tarayya ta bukata.
A kwanakin baya ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi Dangote da mai kamfanin BUA Abdussamad Isyaku Rabiu da su karya farashin siminti.
Sai dai Dangote ya bayyana cewa dala da kudin mota ne ke daga farashin simiti, domin a lokacin da suke siyar da siminti akan N1,300 dala na akan N120 ne.
Saboda haka ko wani buhun siminti ana biya masa kudin mota N800 kuma suna siyar da shi akan N2,350, don haka idan aka cire naira dari takwas daga farashin zai rage N1500 kenan farashin simintin.
A halin da ake ciki, Dangote ya kuma yi karin haske kan inda aka kwana dangane da aiki matatar mai da yake ginawa.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An saki Dino Melaye bayan anyi garkuwa da shi
A tattaunawar da suka yi da manema labarai ya bayyana cewa an kusa kammala aikin matatar man nan bada jimawa ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng