Oshiomhole zai tabbatar da nasarar Buhari a 2019: Fayemi
Gwamnan jihar Ekiti mai jiran gado, Dr Kayode Fayemi yace da nasarar da yayi a ranar 14 ga watan Yuli, 2018, shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Kwamrad Adams Oshiomhole zai sake nasara a zaben jihar Osun mai zuwa da kuma zaben shugaban kasa da za’a yi a ranar 16 ga watan Fabrairun 2019.
Fayemi wadda yayi Magana a jiya a Aubuja a sakatariyar APC na kasa bayan ganawa da Oshiomhole, ya bayyana sauya shekar wasu yan majalisun dokokin kasar a matsayin “damokradiyya a aikace”.
A cewarsa sauya shekarsu bai tada hankalin jam’iyyarsu ba ko kadan, domin sun yarda da kansu da kuma shugabancin jagoransu.
Ya jadadda cewa siyasa ta gaji haka yayinda ake kulle wasu kofofi haka ake bude wasu.
KU KARANTA KUMA: Yayinda yan majalisa da yawa suka sauya sheka a APC, gwamnoni sun yunkura domin ceto jam’iyyar
Tsohon ministan ma’adinai yace ziyarar da ya kai hedkwatar jam’iyyar ba komai bace face ziyarar ban girma. Cewa wannan ne karo na farko day a ziyarci sakatariyar tunda Oshiomhole ya karbi shugabancin jam’iyyar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng