Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Gwamnatin Jihar Niger ta sanar da cewa ta fitar da naira biliyan 2.6 domin ta biya hakkin kudaden ‘yan fansho har su 1,599 daga cikin ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha. Darakta Janar na Hukumar Fansho din ya sanar da hakan.
Kasa da makonni uku kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress ( APC ), mambobin jam’iyyar babin jihar Sokoto sun tsayar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takaran da suke so ya samu tikitin APC.
Dan takaran kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar yayi tattaki zuwa jihar Ekiti domin neman goyon bayan tawagar jihar a babban taron jam’iyyar da za’a gudanar.
Laftanar Janar Tukur Buratai a ranar Talata, 3 ga watan Satumba ya sake bayyana cewa an gurgunta yan ta’addan Boko Haram sannan kuma cewa babu yan ta’adda dake sake kafuwa a Arewa maso gabashin kasar kamar yadda ake rade-radi.
Ronke Ajayi ta sha alwashin siyar da dukkanin kayayyakin ta domin tabbatar da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya siya fam din takara na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin takarar kujerar shugaban kasa a 2019.
Uwargidan shugaban kasa Buhari, Aisha ta halarcin taron hana yaduwar cutar kanjamau na china da Afrika wadda uwargidan shugaban kasar China Farfesa Peng Liyuan ta shirya. Ta kuma samu damar ganawa da matan shugabannin Afrika.
Shugaban hukumar na Zone ‘D’, wadda suka hada da jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Bauchi, Gombe, Plateau, Benue da Nasarawa, Peters Olugboyega, ya bayyana hakan a ranar Litinin, 3 ga watan Satumba a wani taron manema labarai.
Rundunar yan sanda na jihar Enugu sun tabbatar da kama wani shugaban makarantar firamare, Idoko Nathiel mai shekaru 50 a kauyen Mkpamteulo, garin Enugu Ezike kan zargin lalata yara hudu dake karkashin kulawarsa.
Zargin mallakawa mambobin majalisar dokokin kasar dake mulki tikitin tazarce azaben 2019, ya haifar da rikici tsakanin shugaban jham’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da masu niyan takara a fadin jihohin kasar a zabe mai zuwa.
Aisha Musa
Samu kari