Kano Ta Yi Zarra, Ta fi Dukkan Jihohin Najeriya Sababbin Masu Rijistar Katin Zaɓe
- Jihar Kano ce ta zo ta farko a Najeriya wajen sababbin masu rajistar katin zabe a fadin Najeriya baki daya
- Rahoto ya bayyana cewa kokarin wayar da kan jama’a da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi ne ya taimaka wajen samun nasarar
- Matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen wannan nasara, yayin da kwamitin ya bukaci a kara wayar da kai a wasu kananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jihar Kano ta zama jiha mafi yawan sababbin masu rajistar katin zabe a fadin Najeriya gaba daya.
Rahoto ya bayyana cewa jihar ta samu mutum 441,845 da suka yi rajista a shirin rajistar masu kada kuri’a.

Source: Facebook
An bayyana alkaluman ne a cikin rahoton Kwamitin ICT da Tattara Bayanai ya gabatar, karkashin jagorancin Kwamishinan Raya Kiwon Dabbobi, Dakta Aliyu Isa Aliyu, cewar Punch.
Musabbabin nasarar da Kano ta samu
Rahoton da aka fitar ya nuna cewa Kano ta zarce dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, abin da ke nuna karuwar wayewar siyasa.
An ce wannan nasara ta samo asali ne daga ci gaba da wayar da kan jama'a da kuma shirye-shiryen karfafa rajistar masu zabe.
An kuma bayyana cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kafa Kwamitin Karfafa Rajistar Masu Zabe tun shekarar 2025.
Kwamitin ya yi aiki domin karfafa gwiwar mutanen da suka cancanta, musamman matasa, su yi rajista tare da shiga harkokin dimokuradiyya yadda ya kamata.
Bayanan rajistar daga kananan hukumomi 44 sun nuna bambance-bambance, inda Bichi ta jagoranci jerin da sababbin masu rajista 30,806.
Kumbotso ta biyo baya da mutum 18,701, sai Nasarawa mai 18,184, Dawaki Tofa mai 17,748, Bagwai mai 15,808 da Ungogo mai 15,584.
A bangaren da suka fi karancin rajista kuwa, Kunchi ta samu mutum 5,030, Warawa 5,462, Tsanyawa 5,597 da Garun Malam 5,679.

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Tinubu kan batun kafa yan sandan jihohi a Najeriya

Source: Original
Bambancin yankuna birni da na karkara
Rahoton ya lura cewa yankunan birane, musamman a cikin, sun samu yawan rajista fiye da wasu yankunan karkara, cewar Daily Post.
Haka kuma, an bayyana cewa matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen karuwar rajistar, lamarin da ya taimaka wajen nasarar da Kano ta samu.
An yaba musamman ga Karamar Hukumar Bichi, inda aka ce ta yi rawar gani sosai wajen tara sababbin masu rajista a fadin jihar.
Rahoton ya ce Bichi kadai ta bayar da kusan kashi bakwai cikin 100 na jimillar sababbin masu rajista a Kano.
Domin ci gaba da wannan nasara, kwamitin ya ba da shawarar kara wayar da kan jama'a a kananan hukumomin da suka yi kasa wajen rajista.
Abba Kabir ya yabawa salon mulkin Tinubu
A baya, an ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna jin dadinsa kan amfanin da jihar ta samu sakamakon hadin gwiwa da gwamnatin tarayya.
Abba Kabir Yusuf ya bukaci mutanen Kano da su ci gaba da nuna goyon baya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi aiki tukuru domin fadada hadin gwiwar da ke tsakanin gwamnatinsa da gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng

