Rikici ya billo a PDP kan bayar da tikin tazarce ga yan majalisar dokoki

Rikici ya billo a PDP kan bayar da tikin tazarce ga yan majalisar dokoki

Zargin mallakawa mambobin majalisar dokokin kasar dake mulki tikitin tazarce azaben 2019, ya haifar da rikici tsakanin shugaban jham’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da masu niyan takara a fadin jihohin kasar a zabe mai zuwa.

Masu zanga-zanga, wadda suka mamaye sakatariyar jam’iyyar dake Abuja a ranar Litinin, sun bukaci a ja daga tsakanin yan takara ta hanyar gudanar da zaben fidda gwani a fadin jihohin.

Daya daga cikin kungiyoyin dake zanga-zanga daga jihar Kogi sunce bayar da tikitin tazarce kai tsaye ga yan majalisa ya sabama dokar zabe, kundin tsarin mulkin PDP da kuma tsarin jam’iyyar.

Rikici ya billo a PDP kan bayar da tikin tazarce ga yan majalisar dokoki
Rikici ya billo a PDP kan bayar da tikin tazarce ga yan majalisar dokoki
Asali: Twitter

Da take koro jawabi a madadin jam’iyyar Dr Halimat Hamzat, sunce lallai sai an basu dama daidai da kowa ta hanyar yin zaben fidda gwani.

Dr. Hamzat ta ce an gano makircin da jam’iyyar ke kullawa na bayar da tikitin tazarce ga yan majalisa a makon day a gabata lokacin da wani dan takarar kujerar majalisar wakilai ya ziyarci daya daga cikin shugabannin jam’iyyar inda ya hadu da sanatan PDP mai ci.

KU KARANTA KUMA: Taron FOCAC 2018: Manyan abubuwa 5 da Buhari ya fadi a China

A cewar Hamzat sanatan ya fadama dan takarar cewa an bayar da tikitin majalisar dokoki ga dukkanin mambobin majalisar wakilai da na dattawa ga mambobi masu mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel