Dubi Ronke Ajayi wacce ta sha alwashin siyar da dukkanin abunda ta mallaka don siyawa Buhari fam din takara

Dubi Ronke Ajayi wacce ta sha alwashin siyar da dukkanin abunda ta mallaka don siyawa Buhari fam din takara

- Wata mata mai suna Roke Ajayi ta sha alwashin siyar da kayayyakinta donn ganin Buhari ya mallaki fam din takara a APC

- Ta ce da shugabancin Shugaba Buhari da Osinbajo yaran da za'a haifa anan gaba zasu samu ngantaccen rayuwa

- Ronke ta jadadda cewa gwamnatin APC ta cancanci yin tazarce

Wata mata mai shekaru 35 a duniya, Ronke Ajayi ta sha alwashin siyar da dukkanin kayayyakin ta domin tabbatar da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya siya fam din takara na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Legit.ng ta tattaro cewa idan har aka sake zabar Shugaba Buhari da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a 2019, toh babu shakka yaran da za’a Haifa anan gaba zasu samu rayuwa mai inganci.

Dubi Ronke Ajayi wacce ta sha alwashin siyar da dukkanin abunda ta mallaka don siyawa Buhari fam din takara
Dubi Ronke Ajayi wacce ta sha alwashin siyar da dukkanin abunda ta mallaka don siyawa Buhari fam din takara
Asali: Twitter

Tayi imani cewa Buhari ya cancanci yin tazarce akan kujerar mulki saboda tarin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a shekaru uku da yayi akan mulki.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, yan takara a karkashin jam’iyyar APC na ci gaba da nuna dari-dari da shuwagabannin jam’iyyar, biyo bayan tsadar kudin tikitin tsayawa takara da jam’iyyar ta sanar.

KU KARANTA KUMA: 2019: Dalilin da yasa nake son kujerar Dogara – Dan majalisa

An tattaro cewa yan takara a jam’iyyar, da suka nuna sha’awar tsayawa takara a matakin gwamna, majalisun dokoki na kasa da ma shugaban kasa, na bayyana damuwarsu bisa tsadar da tikitin yayi.

Rahotanni sun bayyana cewa yan takarar sun bukaci da a rage kudaden da aka sanya.

A baya bayan nan ne dai kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC, ya fitar da kudin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa akan Naira Miliyan 55, wanda ya haura Naira Miliyan 12 da jam’iyyar PDP ta sanyawa nata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel