Yanzu Yanzu: Rundunar soji sun kashe yan ta’adda, sun samo dabbobi 147 da aka sace a Borno

Yanzu Yanzu: Rundunar soji sun kashe yan ta’adda, sun samo dabbobi 147 da aka sace a Borno

- Sojin Najeriya sun kashe mambobin kungiyar yan ta’addan Boko Haram da dama

- Sojojin sun dawo da dabbobi 147 da yan ta'addan suka sace

- Hakan ya biyo bayan ayyuka biyu da dakarun sojin suka gudanar a kauyukan Jentilo da Gesada na kananan hukumomin Kukawa da Guzamala dake Borno

Rundunar sojin Najeriya sun kashe mambobin kungiyar yan ta’addan Boko Haram da dama a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, kakakin rundunar sojin, Texas Chukwu ya bayyana.

Rundunar ta kuma bayyana cewa ta samo dabbobi 147 daga yan ta’addan dake tsere a jihar Borno.

Chukwu yace an kashe yan ta’addan ne tare da kamun a lokacin wasu ayyuka biyu da dakarun sojin suka gudanar a kauyukan Jentilo da Gesada na kananan hukumomin Kukawa da Guzamala dake Borno.

Yanzu Yanzu: Rundunar soji sun kashe yan ta’adda, sun samo dabbobi 147 da aka sace a Borno
Yanzu Yanzu: Rundunar soji sun kashe yan ta’adda, sun samo dabbobi 147 da aka sace a Borno
Asali: Facebook

Ya ce dakarun sashi 3 na Operation Lafiya Dole da bataliyan hadin gwiwa na 82, sun gudanar da ayyukan kakkaba inda suka kashe yan ta’addan lokacin da suka yi kokarin sace kudade da dabbobi mallakar mutanen kauyen.

KU KARANTA KUMA: Kasar India ta halatta yin luwadi da madigo

Ya cigaba da bayanin cewa kayayyakin da aka kwato daga yan ta’addan sun hada da dabbobi 147, bindigogin AK47 guda biyu.

A cewar Chukwu rundunar sojin sun mayar da dabbobin ga mamalakansu bayan tantancewa da tabbatarwa daga shugaban yankin da jami’an hadin gwiwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel